Yanzu-yanzu: AMCON ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima

Yanzu-yanzu: AMCON ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima

Hukumar kula da kadarorin Najeriya (AMCON) ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima, tsohon na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan bashin da ake bin sa.

Jude Nwauzor, shugaban fannin sadarwar hukumar, ya bayyana hakan a wata takarda da ta fita a ranar Talata.

Ya ce AMCON na bin Galadima da Bedko Nigeria Limited bashin kusan Naira miliyan 900 tun a 2011. Galadima da kamfanin nasa sun yi amfani da kudin ne don siyan kadara daga bankin Unity a 2011.

Yanzu-yanzu: AMCON ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima
Yanzu-yanzu: AMCON ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kotu ta aike wa shugaban gidan yari sammaci a kan hana El-Zakzaky ganin likita

Sai dai a bangarensa, Buba Galadima ya yi magana da BBC Hausa inda ya shaida mata cewa bai karbi kudin kowa ba. Tsohon Sakataren jam’iyyar CPC na kasa, ya koka da wannnan lamari.

A cewarsa, kwangilar shigo da takin zamani aka ba shi a lokacin gwamnatin Ibrahim Shekarau a 2003, amma Galadima ya ce bai yi nasarar samun kudin da zai yi wannan aiki ba.

‘Yan kasuwa sun hana ‘dan siyasar kayan da ya bukata ne saboda hukumomin FBI na kasar Amurka su na binciken wannan banki wanda a karshe ya narke a cikin Unity Bank.

Duk da Galadima bai yi nasarar shigo da kayan ba, daga baya an fito an bayyana masa cewa kudin ruwa ya taru daga bashin da ya bukaci ya karba, duk da cewa kudin ba su shigo hannunsa ba.

Injiniya Galadima ya shaidawa ‘Yan jarida cewa an kai shi kotun tarayya domin a tursasa masa ya biya wannan kudin ruwa na Naira Miliyan 349, kuma Alkali ya bada hukuncin ayi haka.

Sai dai kuma ya daukaka kara inda kotu ta bashi nasara.

Sai kuma daga baya hukumar AMCON ta sake maka shi a wata karamar kotu inda ta samo izinin korar shi daga gidan da ya ke zama. Galadima ya kwatanta mulkin Shugaba Buhari da na Fir'auna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel