Hukumar NAFDAC ta gargadi yan Najeriya kan zuwa teburin Maishayi

Hukumar NAFDAC ta gargadi yan Najeriya kan zuwa teburin Maishayi

Hukumar lura da ingancin abinci da magani wato NAFDAC ta gargadi yan Najeriya kan shan shayi a teburin masu sayar da kayan karin kumallo da aka fi sani da Masu shayi.

Diraktar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta yi gargadin ne a wani hira da tayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a Abuja yau Litinin.

Adeyeye ta ce gargadin ya zamo wajibi saboda an samu labarin cewa masu shayin sun fara gauraya da ruwan bununsy da kwayoyi kafin baiwa kwastamoninsu.

Ta kawo misalin irin kwayoyin da ake sawa irinsu tramadol, Vieteling, Wiwi da sauransu inda ta kara da cewa mutane kan iya rasa rayukansu idan aka gauraya shayi da wadannan muggan kwayoyin.

Tace “A Amurka, mutane da dama sun rasa rayukansu sanadiyar wadannan magungunan. Akwia magungunan da mutum ba zai sha ba idan yana fama da ciwon zuciya.“

Hakazalika ta yi kira da yan Najeriya su guji shan magungunan kara karfin maza saboda illolinsa sa suka tattare da shi.

KU KARANTA Kudu ya kamata a baiwa shugaban kasa a 2023 - El-Rufai

A bangare guda, Kungiyar fafutukan dakile ta'amuni da muggan kwayoyi a Arewa wato Drug Free Arewa Movement, DFAM ta yi kira ga gwamnati ta haramta sana'ar 'Kafada Kemist' a Arewacin NAjeriya domin magance kwaya.

Wata mambar kungiyar, Gambo Wakili, ya bayyana hakan ne yayinda take karanta jawabin da kungiyar ta saki bayan taron yaki da ta'amuni da kwaya cikin matasa da ya gudana a Abuja.

Gambo ta ce ya zama wajibi a kawar da wadannan masu sayar da maganin saboda su ke sayarwa matasa magungunan da suke cutarsu.

Ta yi kira gwamnonin jihohin Arewa 19, sarakunan gargajiya, yan majalisu da masu ruwa da tsaki su sanya hannu wajen yakin magance kwaya da sace-sacen yara.

A cewarta, lissafin da hukumar lissafi ta kasa wato NBS ta fitar kan ta'amuni da kwayoyi ya nuna cewa abin ya yi muni a Arewacin Najeriya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel