Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Adamawa, sun yi mumunan barna

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Adamawa, sun yi mumunan barna

Wasu yan taaddan Boko haram sun hallaka mutane da dama a garin Garkida, wani gari a karamar hukumar Gombi ta jihar Adamawa, The Cable ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa yan taaddan sun kai farmaki garin ne misalin karfe 7 bayan sallan Magariba inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

An bayyana cewa Sojojin da suka fara musayar wuta da yan Boko Haramun sun janye daga baya saboda sun fi su yawa.

Bayan janyewan Sojoji, yan taaddan sun bazama cikin garin inda suka hallaka mutane kuma suka bankwa gidajensu wuta.

A cewar Majiyar: “An ruwan wuta a Garkada yanzu.....An kashe mutane da dama kuma an bankawa gidaje wuta.“

Wani mazaunin garin daban ya tabbatar da hakan inda yace “Mutane sun gudu cikin duwatsu yayinda yan ta“addan ke kona gidajensu“

Wani tsohon shugaban kungiyar yan jaridan Najeriya shiyar Adamawa, wanda mazaunin Garkada ne ya ce lallai ya samu labarin yan Boko Haram sun ci karfin Sojojin dake garin.

Mun kawo muku rahoton cewa a yau jumaa, 21 ga watan Febrairu, 2020 Jaruman Sojojin Najeriya sukayi musayar wuta da yan taaddan Boko Haram a kauyen Latawa, karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe.

Mutan garin sun arce daga muhallansu gudun tsallen Albursai.

Hakazalika, mun kawo muku rahoton cewa Yan taa’ddan Boko Haram sun kai hari yanzu a garin Korongilum dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno a ranar Talata.

Wani jarumin jami’in soja ya rasa kafarsa yayinda aka nemi abokan aikinsa biyu aka rasa yayinda suka taka Bam da wasu yan Boko Haram suka dasa a Korongilum.

An tura Sojoji garin ne da safiyar ranar Laraba domin kawar da yan Boko Haram da suka garin daren Talata.

Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyanawa manema labarai ranar Alhamis cewa rundunar 117 Bataliya dake Chibok sun kusa isa garin Korongilum yayinda Bam ya tashi da motocin da suka dauke da su.

“Sojoji bakwai sunyi matukar jikkata, kuma daya daga cikinsu ya rasa kafarsa“

“Kwamandan bataliyan, Laftanan Kanar SA Yahaya ne ya jagoranci tawagar. Da alamun shi aka nufa da Bam din amma ba ya cikin motar lokacin.“ cewar majiya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel