Gwamnatin tarayya zata gina masana’anta a kowacce mazaba a Najeriya - Minista

Gwamnatin tarayya zata gina masana’anta a kowacce mazaba a Najeriya - Minista

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta kafa akalla masana’anta daya a kowacce mazaba cikin mazabu kashin majalisar dattawa 109 a fadin tarayya.

Karamar Ministar ma’aikatar masana’antu, kasuwanci , da zuba hannun jari, Ambasada Mariam Yalwaji Katagum, ta bayyana haka ne ranar Alhamis a Jihar Kano a yayin da ta kai ziyarar ban girma ga gwamna Abdullahi Ganduje.

Ministar ta ziyarci jihar ne domin kaddamar da cibiyar kanikanci na zamani da ofishoshi a masana’antar koyar da aikin hannu.

`A jawabinta, ta alanta shirin kafa masana’antu sarrafa kayan noma a sassan Najeriya shida, kuma an fara tattauna lamarin a zaman mako-mako na majalisar zantarwan tarayya.

Tace ”Ya nada muhimmanci in fara janyo hankalin mutane kan cewa nan da shekara mai zuwa, zaa kaddamar da wadannan masana’antun sarrafa kayayyakin gonan kuma dukkan sassan kasa zasu samu nan da 2023”

A nasa jawabin, Gwamnan jihar kano, Abdulahi Ganduje ya bayyana cewa Kano gari ne na kasuwanci da masana’antu, kuma za’a kara samar da masana’antu a Jihar

KU KARANTA Sojoji na artabu da yan Boko Haram yanzu haka a Yobe

Gwamnatin tarayya zata gina masana’anta a kowacce mazaba a Najeriya - Minista
Gwamnatin tarayya zata gina masana’anta a kowacce mazaba a Najeriya - Minista
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya zata gina masana’anta a kowacce mazaba a Najeriya - Minista
Gwamnatin tarayya zata gina masana’anta a kowacce mazaba a Najeriya - Minista
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel