Harin Chibok: Soja ya rasa kafarsa, an nemi biyu an rasa

Harin Chibok: Soja ya rasa kafarsa, an nemi biyu an rasa

Wani jarumin jami’in soja ya rasa kafarsa yayinda aka nemi abokan aikinsa biyu aka rasa yayinda suka taka Bam da wasu yan Boko Haram suka dasa a Korongilum, wani gari dake karamar hukumar Chibok, jihar Borno, TheCable ta ruwaito.

An tura Sojoji garin ne da safiyar ranar Laraba domin kawar da yan Boko Haram da suka garin daren Talata.

Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyanawa manema labarai ranar Alhamis cewa rundunar 117 Bataliya dake Chibok sun kusa isa garin Korongilum yayinda Bam ya tashi da motocin da suka dauke da su.

“Sojoji bakwai sunyi matukar jikkata, kuma daya daga cikinsu ya rasa kafarsa“

“Kwamandan bataliyan, Laftanan Kanar SA Yahaya ne ya jagoranci tawagar. Da alamun shi aka nufa da Bam din amma ba ya cikin motar lokacin.“ cewar majiya

Wata majiyar daban ta bayyana cewa “Da alamun yan taaddan Boko Haram sun dasa bama-bamai ne a wurare da dama cikin garin, kuma mutan garin na guduwa daga muhallansu.“

Daya daga cikin mazauna garin ya bayyana cewa: “A yanzu haka, babu Sojoji a nan. Wadanda aka turo sun gamu da Bam jiya, har yanzu ba“a turo wasu ba“

KU KARANTA: Yadda 'Yahoo boys' suka yiwa mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa mumunan kisa a Abuja

Mun kawo muku rahoton cewa Yan taa’ddan Boko Haram na kan kai hari yanzu a garin Korongilum dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Wani mazaunin garin ya bayyanawa manema labarai cewa yan ta’addan sun shiga garin ne misalin karfe 6 na yamma kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Hakazalika suna bankawa gidajen mutane wuta.

Yace “Dawowar mutane gida daga gonakinke da wuya, sai yan taaddan suka shigo. Sun samu shiga ne ta Forfor, kuma mutane na guduwa yanzu.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel