Tashin hankali: An tsinci gawar mutumin da yayi kokarin kashe shugaban kasa

Tashin hankali: An tsinci gawar mutumin da yayi kokarin kashe shugaban kasa

- Mawakin yabo na addinin Kirista a kasar Rwanda mai suna Kirito Mihigo ya kashe kan shi

- A 2015, an kama mawakin da laifin yunkurin kashe Shugaban kasa Paul Kagame amma sai aka yi mishi rangwame a 2018

- A makon da ya gabata ne aka damke shi bayan yayi yunkurin barin kasar ta iyakar Burundi, wanda hakan ya sabawa sharuddan rangwamen

Mawakin yabo na addinin Kirista a kasar Rwanda, Kirito Mihigo, wanda aka taba kamawa da laifin kokarin kashe Shugaban kasa Paul Kagame ya rasu.

Kamar yadda 'yan sanda suka sanar, Mihigo mai shekaru 38 ya kashe kan shi ne a yayin da yake tsare wajen 'yan sanda.

Tashin hankali: An tsinci gawar mutumin da yayi kokarin kashe shugaban kasa
Tashin hankali: An tsinci gawar mutumin da yayi kokarin kashe shugaban kasa
Asali: Facebook

An yanke mishi hukuncin shekaru 10 a gidan yari ne bayan da aka kama shi da laifin hada kungiyar 'yan daba, hada kai wajen kisan kai da kuma hada kai don cutar da gwamnati tare da Shugaban kasa.

KU KARANTA: Hoton fim din Indiya na farko da aka yi da bakar fata mai suna 'Namaste Wahala' ya fita

An yafewa Mihigo a 2018 amma sai aka kara kama shi a makon da ya gabata yayin da yake kokarin tsallakawa zuwa Burundi.

Hukumomi sun sanar da cewa wannan karantsaye ne ga sharuddan rangwame, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito.

"Jami'an tsaro sun adana shi na kwanaki uku yayin da suke binciken dalilin tsallake iyakar ba tare da bin ka'ida ba da kuma zargin cin hanci", mai magana da yawun 'yan sandan Eric Kabera ya sanar a takardar.

Ya kara da cewa, an bar Mihigo ganawa da iyalansa tare da lauyansa ko a lokacin da yake tsare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel