Da duminsa daga kotun koli: An dage zaman sake duba shariar Zamfara zuwa 2 ga Maris

Da duminsa daga kotun koli: An dage zaman sake duba shariar Zamfara zuwa 2 ga Maris

Kotun Kolin Najeriya ta dage zaman sauraron bukatar sake duba shariar zaben gwamnan jihar Zamfara da bangaren AbdulAziz Yari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da bangaren suka shigar kan bangaren Sanata Kabiru Marafa.

Bangaren Yari ta jamiyyar APC a jihar Zamfara ta bukaci kotun ta sake duba hukuncin fitittikan dukkan wadanda aka zabe karkashin lemarta a zaben 2019.

Yayinda aka hallara a kotu yau, shugaban Alkalan tarayya, CJN Tanko Muhammad, wanda ya jagoranci kwamitin Alkalan lamarin yace ba zai yiwu a saurari karar ba saboda dukkan bangarorin basu samu takardar kara ba.

Lauyan bangaren Yari, Robert Clarke, lauyan bangaren Marafa, Mike Ozekhome, da lauyan INEC, Tanimu Inuwa, sun amince a dage karar.

An dage zuwa ranar 2 ga Maris, 2020.

Da duminsa daga kotun koli: An dage zaman sake duba shariar Zamfara zuwa 2 ga Maris
Da duminsa daga kotun koli: An dage zaman sake duba shariar Zamfara zuwa 2 ga Maris
Asali: Facebook

KU KARANTA Dalilin da yasa Buhari ba zai canza hafsoshin tsaro ba - Fadar shugaban kasa

Jamiyyar APC a jihar ta shigar da kara ne ta lauyanta, Robert Clarke, inda ta bukaci kotun ta sake duba hukuncin da ta sake ranar 24 ga Mayu, 2019 na sallamar dukkan wadanda suka lashe zabe karkashin APC saboda basu gudanar da zaben fidda gwani ba.

Za ku tuna cewa ana saura kwanaki biyar rantsar da sabon gwamnan jihar Zamfara, kwamitin Alkalan kotun koli biyar karkashin CJN Tanko Muhammad sun yi ittifakin cewa jamiyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga dokokin jamiyyar saboda haka dukkan kuriun da APC ta samu a zaben ya zama banza.

Sakamakon haka, wanda ya zo na biyu a zaben, Bello Matawalle na PDP ya zama zakaran zabe kuma a ranstar da shi matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel