Yanzu-yanzu: Jamian tsaro sun mamaye kotun koli yayinda ake shirin sake duba shariar Imo da Zamfara

Yanzu-yanzu: Jamian tsaro sun mamaye kotun koli yayinda ake shirin sake duba shariar Imo da Zamfara

Jamian tsaro sun mamaye kotun koli a yau Talata yayinda Alkalan kotun ke shirin sake duba shari'u biyu da suka yanke na zaben gwamnan jihar Imo da Zamfara.

Ihedioha ya bukaci kotun koli ta sake duba hukuncin da ta yanke na cireshi matsayin gwamnan jihar Imo yayinda jamiyyar APC a jihar Zamfara ta bukaci kotun ta sake duba hukuncin fitittikan dukkan wadanda aka zabe karkashin lemarta a zaben 2019.

Za ku tuna cewa Kotun kolin Najeriya da ta fititiki gwamnan PDP, Emeka Ihedioha, kuma ta baiwa na APC, Hope Uzodinma.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

KU KARANTA Dalilin da yasa Buhari ba zai canza hafsoshin tsaro ba - Fadar shugaban kasa

A jihar Zamfara kuwa, Jamiyyar APC a jihar ta shigar da kara ne ta lauyanta, Robert Clarke, inda ta bukaci kotun ta sake duba hukuncin da ta sake ranar 24 ga Mayu, 2019 na sallamar dukkan wadanda suka lashe zabe karkashin APC saboda basu gudanar da zaben fidda gwani ba.

Za ku tuna cewa ana saura kwanaki biyar rantsar da sabon gwamnan jihar Zamfara, kwamitin Alkalan kotun koli biyar karkashin CJN Tanko Muhammad sun yi ittifakin cewa jamiyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga dokokin jamiyyar saboda haka dukkan kuriun da APC ta samu a zaben ya zama banza.

Sakamakon haka, wanda ya zo na biyu a zaben ya zama zakaran zabe kuma a ranstar da shi matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara.

Abin mamaki a wannan sharia shine dan jamiyyar APC, Sanata Kabiru Marafa, ne ya shigar da wannan karar kan jamiyyarsa wanda ya kaisu ga biyu babu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel