Dalilin da yasa Buhari ba zai canza hafsoshin tsaro ba - Fadar shugaban kasa

Dalilin da yasa Buhari ba zai canza hafsoshin tsaro ba - Fadar shugaban kasa

Kungiyoyi daban-daban a fadin tarayya da masu sharhi kan lamuran yau da kullum basu gushe ba suna kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro saboda sun yi kasa a gwiwa.

Hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane a Arewa maso yamma ya karu yayinda yan taaddan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas suka addabi alummar Arewa maso gabas ba dare, ba rana.

Hari mafi muni na karshe da suka kai shine a garin Auno, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda suka kashe akalla mutane 30 kuma suka lalata dukiyoyin miliyoyin naira.

A ranar Litinin, an shirya gudanar da zanga-zanga kan tilastawa Buhari sallamar hafsoshin amma gwamnati ta ce wasu yan adawa ne suka shirya.

Dalilin da yasa Buhari ba zai canza hafsoshin tsaro ba - Fadar shugaban kasa
Dalilin da yasa Buhari ba zai canza hafsoshin tsaro ba - Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Dukkan hafsoshin tsaron sun wuce shekaru hudu da doka ta tsara ga Soja yayi a sabis. Sun hada da Janar Abayomi Olonishakin (Babban hafsan tsaro), Laftanan Janar Tukur Buratai (Shugaban sojojin kasa), Air Marshal Sadique Abubakar (Shugaban mayakan sama) da Vice Admiral Ibok Atas (shugaban sojin ruwa).

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya yi bayani ranar Lahadi cewa ba cire hafsoshin tsaro magance matsalar tsaron da Najeriya ke fama da shi ba.

Garba Shehu yace “Cire ko korar hafsoshin tsaro ba zai kawar da abubuwan da muke fuskanta ba. Ko mu yarda ko kada mu yarda, mun cikin halin yaki. “

“Shugaban kasa kuma babban kwamandan Sojin Najeriya na hangen abubuwan da wasu basu iya hange. Shi yasa ya kamata a yi masa uzuri. “

“Ta yaya zasu ce shugaban kasan bai damu ba? bayan zuciyarsa na kan yadda zai kasar nan. Wadanda basu san abinda gwamnati keyi bane suke cewa shugaban kasa bai damu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel