Bayan yanke hukunci, Kotun koli za ta zauna kan korafin Ihedioha da Lyon ranar Talata

Bayan yanke hukunci, Kotun koli za ta zauna kan korafin Ihedioha da Lyon ranar Talata

Kotun kolin tarayya ta zabi ranar Talata, 18 ga watan Febrairu domin sauraron korafin Emeka Ihedioha, tsohon gwamnan jihar Imo da David Lyon, wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa kafin kwace kujerar ana saura kwanan daya a rantsar da shi.

Kakakin kotun koli, Festus Akande, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Asabar. The Cable ta ruwaito.

“Hakan gaskiyane. Za’a saurari karan Bayelsa a ranar (Talata)” Ya bayyana a waya.

Ihedioha ya bukaci kotun koli ta sake duba hukuncin da ta yanke na cireshi matsayin gwamnan jihar Imo yayinda shi kuma David Lyon ya bukaci kotun ta sake duba dalilin da yasa aka hanashi kujerarsa duk da ya ci zabe.

Bayan yanke hukunci, Kotun koli za ta zauna kan korafin Ihedioha da Lyon ranar Talata
Kotun koli
Asali: Depositphotos

Za ku tuna cewa Kotun kolin Najeriya da ta fititiki gwamnan PDP, Emeka Ihedioha, kuma ta baiwa na APC, Hope Uzodinma.

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

Saboda haka, ta yi watsi da sanarwan INEC na baiwa Emeka Ihedioha nasara.

A Bayelsa kuwa, Ana saura awanni kasa da 24 da rantsar da sabon gwamna, kotun koli a ranar Alhamis ta fitittiki David Lyon a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa tare da mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo matsayin wadanda suka lashe zaben 16 ga Nuwamba 2019.

Alkali Ejembi Eko, wanda ya karanto da shari'ar ya yi amfani da shari'ar babbar kotun tarayya dake Abuja da ta hana Degi-Eremiwoyo takara a zaben gwamnan.

Kotun kolin ta tabbatar da shari'ar karamar kotun cewa zababben mataimakin gwamnan ya aikata laifi wajen gabatar da kwalin bogi ga hukumar INEC.

Kwamitin Alkalan kotun koli kan karar karkashin jagorancin, Mary Odili, sun yi ittifakin cewa mutum bai cancanci takara a zabe ba muddin ya gabatar da takardun boge domin zaben.

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta shigar da kara kotu kan zargin gabatar da takardun boge da take yiwa dan takarar kujerar mataimakin gwamnan APC, Degi-Eremienyo.

Sun tuhumceshi da gabatar da sunayen daban-daban guda biyar matsayin sunayensa cikin kwalayen karatunsa.

PDP ta ce sunan zababben mataimakin gwamnan dake cikin kwlain karatun firamarensa ya banbanta da na sakandare hakazalika na jami'a.

Ga jerin yadda sunayensa sukea kwalayen:

Kwalin karatun Firamare - Degi Biobara

Kwalin karatun Firamare - Adegi Biobarakumo

Kwalin karatun Jami'a- Degi Biobarakuma

Kwalin karatun Jami'a MBA - Degi Biobarakuma Wangaha

Sunansa a zaben 2019 - Degi-Eremienyo Biobarakuma

Wannan shine dalilin da ya sa kotun koli ta fitittiki zababben gwamnan da mataimakinsa saboda tikitin da sukayi takara daya ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel