Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatar da Modibbo-Kawu a matsayin shugaban NBC
Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Ishaq Moddibo-Kawu a matsayin Direkta Janar na Hukumar Watsa Labarai ta kasa NBC kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito a ranar Juma'a.
Majiyar Legit.ng ta gano cewa an dakatar da shi ne bisa shawarar da Hukumar Yaki da Masu Aikata Rashawa, ICPC, ta bayar ta ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Majiyar ta ce wasikar ta yi umurnin babban direktan a hukumar ya maye gurbin Moddibo-Kawu kafin a kammala binciken da ake gudanar wa a kansa.
"Don haka, Armstrong Idachaba, direktan sashin kula da watsa labarai zai kama aiki a matsayin shugaba na rikon kwarya," in ji majiyar.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48
Wani ma'aikacin NBC da ba a bawa izinin yin magana da kafafen watsa labarai ta shaidawa majiyar Legit.ng ya ce tuni Moddibo-Kawu ya kwashe kayayyakinsa daga ofishinsa.
Idan ba a manta ba dai ana ICPC na bincike a kan zargin damfara ta Naira biliyan 2.5 da aka ce an biya Pinnacle Communications Ltd a matsayin kudin da za su fara aikin sauya tsarin watsa labarai zuwa na zamani wato Digital.
An gano cewa tun a watan Satumban 2019 ne hukumar ta ICPC ta bayar da shawarar a dakatar da Modibbo-Kawu a cikin wasikar da ta aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng