Yan zanga-zanga sun kai hari gidan sabon gwamnan Bayelsa, sun lalata dukiya

Yan zanga-zanga sun kai hari gidan sabon gwamnan Bayelsa, sun lalata dukiya

Fusatattun masu zanga-zanga da ake kyautata zaton yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun kai hari gidan zababben gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, kan nasarar da kotun koli ta bashi bayan sallamar David Lyon na APC.

Yan zangan-zangan sun bazama lalata dukiyoyin jigogin jam'iyyar PDP a a babbar birnin jihar Yenegoa.

Sun fasa gilasan motocin da ke ajiye cikin gida bayan balla kofofi da tagogin dake ciki.

Hakazalika sun kai farmaki dakin karatun dan majalisar wakila mai wakiltar Yenegoa da Kolokuma/Opokuma, Steve Azaiki, sakatariyar PDP da kuma gidan Rediyon jihar.

Mun kawo muku rahoton cewa Zanga-zanga ya barke a sassan Yenegoa, babbar birnin jihar Bayelsa kan shari'ar kotun kolin tarayya da ta hana rantsar da Cif David Lyon, a matsayin gwamnan jihar.

Dubunnan mata sun tare manyan hanyoyin jihar domin inda suka lashi takobin cewa babu wanda za'a rantsar gwamnan jihar Bayelsa yau.

Ana saura awanni kasa da 24 da rantsar da sabon gwamna, kotun koli a ranar Alhamis ta fitittiki David Lyon a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa tare da mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo bayan sun lashe zaben 16 ga Nuwamba 2019.

Alkali Ejembi Eko, wanda ya karanto da shari'ar ya yi amfani da shari'ar babbar kotun tarayya dake Abuja da ta hana Degi-Eremiwoyo takara a zaben gwamnan.

Kotun kolin ta tabbatar da shari'ar karamar kotun cewa zababben mataimakin gwamnan ya aikata laifi wajen gabatar da kwalin bogi ga hukumar INEC.

Kwamitin Alkalan kotun koli kan karar karkashin jagorancin, Mary Odili, sun yi ittifakin cewa mutum bai cancanci takara a zabe ba muddin ya gabatar da takardun boge domin zaben.

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta shigar da kara kotu kan zargin gabatar da takardun boge da take yiwa dan takarar kujerar mataimakin gwamnan APC, Degi-Eremienyo.

Sun tuhumceshi da gabatar da sunayen daban-daban guda biyar matsayin sunayensa cikin kwalayen karatunsa.

PDP ta ce sunan zababben mataimakin gwamnan dake cikin kwalin karatun firamarensa ya banbanta da na sakandare hakazalika na jami'a.

Ga jerin yadda sunayensa sukea kwalayen:

Kwalin karatun Firamare - Degi Biobara

Kwalin karatun Firamare - Adegi Biobarakumo

Kwalin karatun Jami'a- Degi Biobarakuma

Kwalin karatun Jami'a MBA - Degi Biobarakuma Wangaha

Sunansa a zaben 2019 - Degi-Eremienyo Biobarakuma

Wannan shine dalilin da ya sa kotun koli ta fitittiki zababben gwamnan da mataimakinsa saboda tikitin da sukayi takara daya ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel