Harin Boko Haram: Majalisar dattawa ta umurci Sojoji su kafa matsugunni a Auno

Harin Boko Haram: Majalisar dattawa ta umurci Sojoji su kafa matsugunni a Auno

A ranar Alhamis, majalisar dattawar tarayya ta umurci hukumar Sojin Najeriya ta kafa matsugunni a garin Auno domin kare matafiyan dake bin hanyan.

Majalisar ta bada wannan umurnin ne bayan harin da Boko Haram ta kai Auno inda akayi asarar rayuka 30 da dukiyoyi biliyoyi.

Sanata mai wakiltan Borno ta tsakiya, Kashim Shettima, ya bukaci majalisar ta kaddamar da bincike kan harin saboda da alamun akwai cikin nadi.

Harin Boko Haram: Majalisar dattawa ta umurci Sojoji su kafa matsugunni a Auno
Harin Boko Haram: Majalisar dattawa ta umurci Sojoji su kafa matsugunni a Auno
Asali: UGC

A jiya, Shugaba Muhammadu Buhariya dira Borno ne daga kasar Habasha inda ya kwashe kwanaki biyar a taron kasashen nahiyar Afrika.

Misalin karfe 1 na rana gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya karbi bakuncin shugaban kasan tare da ministan walwala, Sadiya Umar Farouk da NSA, Babagana Munguno.

Daga nan ya garzaya fadar mai martaba Shehun Borno, Abubakar ElKanemi, sannan ya tafi gidan gwamnatin jihar domin jin abinci kafin ya fita daga jihar.

Buhari ya koma babbar birnin tarayya Abuja bayan ziyarar jajen da ta'azziyar da ya kai jihar kan kisan akalla mutane 30 a garin Auno, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Lahadi.

Buhari ya bar Borno misalin karfe 4 bayan la'asar ba tare ziyartar garin Auno, inda aka kashe mutanen ba ko gaishe da wadanda suka jikkata kuma suke kwance asibiti ba.

Mun kawo muku rahoton cewa akalla mutane biyar sun jikkata yayinda Boko Haram sukayi kokarin shiga Maiduguri jiya bayan zuwan shugaba Muhammadu Buhari jihar.

An tattaro cewa yan ta'addan sun shiga garin Maiduguri ne bayan Sallar Isha ta Addawari, unguwar Jiddari Polo inda suka harba roka da ya jikkata mutane 5.

Wani mazauni, Ali Maji Bukar, ya bayyana cewa na garzaya da wadanda suka raunata Asibitin jihar domin jinya.

"Bamu san abinda ya faru ba. Sai muka fara jin harbe-harbe a bayan gari da kuma hanyar Damboa." Yace

Sanda Bunu, wanda mazaunin Jiddari Polo ne ya ce bai ka yan ta'addan ba amma ya riga harsasai na yawo a sama.

"Jami'an tsaro sun zaburo da wuri kuma suka kawar da yan ta'addan amma har yanzu mutane na bakin hanya." Yace

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel