Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari

Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya bada sharadin sakin sauran 'yan matan Chibok da har yanzu suke hannunsa bayan da yayi garkuwa da su.

Sama da 'yan mata 100 ne daga cikin 276 da aka sace a makarantar sakadiren 'yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno tun 2014 ke hannun 'yan Boko Haram din.

A wani bidiyo da shugaban Boko haram din ya saki kasa da sa'o'i 24 da zuwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar Borrno, Shekau ya ce zasu saki 'yan matan ne kadai idan gawamnatin tarayya ta saki 'yan kungiyar da ke hannunsu a tsare.

Ya kara da bukatar Shugaba Buhari da kada ya kuskure ya kara zuwa jihar Borno don kuwa a cewarsa kungiyarsa a shirye take.

Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari
Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zaku fada cikin babban 'garari' matukar baku bawa gwamnati goyon baya ba - Buhari ya fada wa matasa

Shekau ya ce 'yan ta'addan zasu hari shugaban kasar matukar ya kara komawa Borno.

Idan zamu tuna dai, mayakan Boko Haram din sun hari jihar sa'o''i kadan bayan da shugaba Buhari ya kammala ta'aziyyar wadanda suka kashe a Auno da ke Maiduguri a ranar Lahadi.

"Buhari ya zo Maiduguri yana ikirarin shi mutumin arziki ne. Toh kada ya kuskure ya kara yin hakan," Shekau ya ce a harshen Hausa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel