Hukuma ta yi kwarmato game da shirin kai ma majalisa harin ta’addanci

Hukuma ta yi kwarmato game da shirin kai ma majalisa harin ta’addanci

Hukumar majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwarta game da yiwuwar kungiyar ta’adda ta kaddamar da harin ta’addanci a majalisa, kamar yadda wani babban jami’in hukumar ya bayyana.

Daily Trust ta ruwaito wannan jami’I da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Da gaske ne, mun samu mummunan rahoton tsaro dake bayyana cewa majalisar dokokin Najeriya na daga cikin wuraren da yan ta’adda ke shirin kaddamar da hari, kuma ba na wasa bane.”

KU KARANTA: A shirye nake na sadaukar da rai na domin kawo zaman lafiya a Arewa maso gabas – Dan majalisa

Hukuma ta yi kwarmato game da shirin kai ma majalisa harin ta’addanci
Majalisa
Asali: UGC

Jami’in yace suna yawan samun bakin fuskoki dake shiga cikin majalisa a yan kwanakin nan, kuma hakan ya zama abin damuwa ga hukumar majalisar, kamar yadda ya shaida ma majiyar Legit.ng.

Jami’in ya kara da cewa a lokutta da dama da zarar jami’an hukumar ko jami’an tsaro sun tunkari wadannan bakin fuskoki game da dalilin zuwansu majalisar sai su ce sun zo wurin wakilansu ne, bugu da kari jami’an tsaron majalisar sun yi karanci.

Ya cigaba da cewa duk da cewa sun dauki matakai da dama da suka kamata, amma masu ruwa da tsaki a majalisar basa bayar da goyon bayan da ya kamata.

Shi ma daraktan hulda da jama’a na majalisar, Yahaya Dan Zaria ya bayyana damuwarsa game da halin da ake ciki, amma yace suna daukan matakan shawo kan fargabar.

A kwanakin baya ma akawun majalisar, Mohammed Ataba Sani Omolori ya kafa wata kwamitin tsaro wanda ta bayar da shawarar a samar da jami’an tsaro na musamman masu dauke da bindigu domin tsaron majalisar.

A wani labarin kuma, an shiga cikin tashin hankali da dimuwa yayin da wata mummunan gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo dake garin Abekuta, babban birnin jahar Ogun.

Gobarar ta tashi ne a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu, da misalin karfe 9:30 a gidan dake unguwar Ita-Eko dake cikin garin Abekuta, sai dai shaidun gani da ido sun bayyana cewa lantarki ne ya janyo gobarar.

Da kyar da sudin goshi makwabta da ma’aikatan gidan suka samu nasarar kashe wutar bayan sun mata taron dangi bayan sun kwashe kimanin awa daya suna fama da ita. Shaidun sun bayyana cewa wutar ta yi ta tashi daga wani sashi zuwa wani sashin gidan saboda iskar bazara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel