Ka aureni ko in rasa raina - Budurwa ta fadi warwas a titi (Bidiyo)

Ka aureni ko in rasa raina - Budurwa ta fadi warwas a titi (Bidiyo)

-Bidiyon wata budurwa kwance kasa warwas a kan titin yayin da ababen hawa ke wucewa ya ba mutane mamaki

- Kamar yadda aka gani a bidiyon, budurwa tayi hakan ne don neman soyayyar saurayinta wanda ke cikin bdiyon yana faman fada

- Kamar yadda masu wucewa suka tsaitsaya, haka masu ababen hawa suka tsaya suna kallonta tare da kokarin kawar da ita

Wani bidiyon budurwa kwance warwas a kan titi a gaban saurayi tamkar ta mutu ya ba mutane mamaki.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta wallafa bidiyon, an ga budurwar kwance kasa tamkar matatta inda wasu masu ababen hawa ke tsayawa tare da jama'a.

Duk a cikin bidiyon dai, an ga saurayin na hargowa tare da cewa "dole ne soyayyar ko kuma dole ne auren?"

DUBA WANNAN: A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

Har ila yau dai, wani saurayin da alamu suka bayyana shine ya dauka wannan bidiyon an ji yana cewa "Wannan ita kuwa me take bukata? Ku kawar da ita daga kan titi yadda take kamar ta mutu."

Kamar yadda hausawa ke fadi, soyayya dai gamon jini ce. Amma duban irin zankadediyar budurwa da ke cikin bidiyon tana niyyar mutuwa a kan saurayi, zamu iya cewa wannan karin maganar ta bahaushe gaskiya ce.

Amma idan so cuta ne, ai hakuri magani ne. Akwai wadanda zasu iya kashe ko nawa ne don samunta ta zama abokiyar rayuwarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel