Coronavirus: An gwada mutane uku - Ministan Lafiya, Osagie Enahire ya bayyana a Kano

Coronavirus: An gwada mutane uku - Ministan Lafiya, Osagie Enahire ya bayyana a Kano

Ministan Lafiya, Dakta Osagie Emmanuel Enahire, a ranar Laraba a jihar Kano ya tabbatar da cewa an gwada mutane uku da ake zargi da daukan cutar Coronavirus a Najeriya kuma an samu basu da cutar.

Ministan ya bayyana hakan ne yayinda yake bude taron makon kiwon lafiya a gidan gwamnatin jihar Kano, inda ya tabbatar da cewa akwai cibiyoyi uku da aka shirya musamman domin gwada mutanen da ake zarginsu da cutar.

Ya kara da cewa za'a kaddamar da asibitin tafi da gidanka a Abuja kwanan nan.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da matakan bincike a dukkan hanyoyin shiga Najeriya domin tantance dukkan fasinjojin da ke shigowa Najeriya domin tabbatar da cewa babu mai dauke da cutar da zai samu damar shigowa kasar.

A taron, Ehanire ya ce gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, lambar yabon gwarzon kiwon lafiyan fari a Najeriya.

Ganduje ne mutum na biyu da zai samu wannan lambar yabon bayan shekaru 27.

Dakta Enahire yace an baiwa Ganduje wannan lambar yabo ne saboda irin rawar ganin da yake takawa wajen samar da kiwon lafiya a jihar.

Coronavirus: An gwada mutane uku - Ministan Lafiya, Osagie Enahire ya bayyana a Kano
Coronavirus: An gwada mutane uku - Ministan Lafiya, Osagie Enahire ya bayyana a Kano
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Abuja, Kano, Legas, Cross River, Akwa Ibom, Port Harcourt, Enugu, Delta da Bayelsa matsayin jihohin da ya kamata a shirya matakan tsaro idan cutar Coronavirus ta bulla a Najeriya.

Babbar jami'ar WHO, Dhamari Naidoo, ta bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata a taron horar da yan jarida kan cutar Coronavirus.

Tace: "Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Najeriya matsayin kasa mai mugun hadarin kamuwa da cutar saboda yawan sufuri tsakanin kasar Sin da Najeriya."

Ta ce WHO na aiki kan karfafa tsaro a iyakokin shiga Najeriya da kuma taimakawa wajen gano zafin jiki da fuskokin masu shigowa.

Dhamari Naidoo ta kara da cewa an sanar da dukkan kamfanonin jiragen sama su yi kyakkyawan lura da masu shigowa Najeriya daga Sin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel