Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)

Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)

Sananne kuma mashahurin marubuci, Wole Soyinka da kuma Sanata Shehu Sani sun isa babbar kotun tarayya da ke Abuja don kallon shari'ar Omoyele Sowore, makirkirin juyin juya-hali.

Soyinka ya isa kotun ne da karfe 8:50 na safiyar yau Laraba kafin isowar Sowore kotun.

Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)
Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)
Asali: Twitter

Sowore da Olawale Bakare ana zarginsu ne a kan laifuka bakwai da suka hada da damfara, batanci ga shugaban kasa da sauransu, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)
Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)
Asali: Twitter

Jami'an hukumar tsaro ta fararen kaya ce ta cafke shi a ranar 3 ga watan Augusta sakamakon zanga-zangar da suka shirya a fadin kasar nan.

An sake shi ne bayan da yayi kwanaki 124 a wajen hukumar. Sun kuwa kara cafke shi kasa da sa'o'i 24 bayan sakin shi a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)
Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)
Asali: Twitter

Daga bisani kuwa an sake shi ne a ranar 24 ga watan Disamba 2019, ana gobe bikin Kirsimetin shekarar tare da Sambo Dasuki, wanda ya fi shi dadewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel