Buhari ya fi kowa fahimtar matsalar tsaron da Najeriya ke fama da shi – Buratai

Buhari ya fi kowa fahimtar matsalar tsaron da Najeriya ke fama da shi – Buratai

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen daukan matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take.

Buratai ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar TheCable, Thisday da kuma gidan talabijin na Arise a ranar Talata, 11 ga watan Feburairu a jahar Legas.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: Sule Lamido ya shawarci Buhari game da matakin daya kamata ya dauka

A kwanakin baya ne majalisar dokokin Najeriya ta nemi Buhari ya sallamki kafatanin hafsoshin tsaron Najeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin gazawarsu wajen kare rayukan yan Najeriya, duba da sake farfadowar da Boko Haram ta yi.

Da wannan ne babban hafsan Sojan, Laftanar Janar Tukuru Tusuf Buratai yace: “Ba tare da kalubalantar ikon majalisa ba, amma sallamar hafsoshin tsaro ba shi bane hanyar da zai warware matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da ita.”

Buratai ya kara da cewa Buhari na sane da halin da ake ciki, kuma shi ne mai dakin, shi ya san inda ke masa yoyo, haka zalika shi kadai ne zai iya yanke hukuncin da ya kamata game da lamarin.

“Ban so yin magana a kan wannan lamari ba, saboda lamari ne daya shafeni kai tsaye, amma na sani duk abinda ya faru babban kwamanda shi ya san halin da ake ciki, kuma shi ne zai iya alkalanci saboda ya san inda matsalolin suke, ina ganin kamata ya yi a barshi ya yanke hukunci, ba wai a dinga ingiza shi ba.

“Muna cikin wani yanayi mai sarkakiya ne, wanda ba abin wasa bane, shi yasa idan ka ce a sallami wasu shuwagabanni a Soja muke mamaki, saboda ai baka magance matsalar ba, ba wai na fadi haka bane don saboda ni ne babban hafsan Sojan kasa, don haka bana so a cire ni.

“A’a, lamarin ya wuce haka, wannan abu ne daya shafi kasa, ya shafi kishin kasa, masu kira a tsige hafsoshin tsaro ai daga cikinmu su ke, su ya kamata su fi daga murya game da abubuwan da ake yi ba daidai ba” Inji shi.

Haka zalika Buratai ya musanta batun cewa a shekarar 2009 aka fara Boko Haram, inda yace an fi shekara 30 ana watsa akidar Boko Haram a cikin al’umma, don haka abu ne mai wuya murkushe akidar gaba daya.

Ya kara nanata cewa Sojoji sun ci galaba a kan Boko Haram saboda a yanzu babu wani yankin Najeriya dake karkashin ikon su, shi yasa suka koma kai hare haren sari ka noke don farfaganda, don haka ya yi kira ga yan jaridu da kada su taimakesu a aikin watsa farfagandar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel