Ta bayyana: Sojojin Amurka 100 sun kamu da ciwon kwakwalwa sakamakon harin Iran

Ta bayyana: Sojojin Amurka 100 sun kamu da ciwon kwakwalwa sakamakon harin Iran

Hukumar Sojin Amurka na shirin bayyanawa duniya cewa yawan Sojojinta da suka samu ciwon kwakwalwa sakamakon harin da kasar Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraqi ya karu da kusan kashi 50, Reuters ta ruwaito.

Jami'an Sojin Amurkan da suka bukaci a sakaye sunayensu sun bayyana cewa sama da Sojoji 100 suka kamu da ciwon kwakwalwa sabanin 64 da aka ruwaito a watan Junairu.

Hedkwatan hukumar, Pentagon, ta ki tsokaci a kan lamarin duk da cewa a baya ta yi hasashen cewa akwai yiwuwan karuwar Sojin da zasu samu matsalar kwakwalwa.

Ta bayyana: Sojojin Amurka 100 sun kamu da ciwon kwakwalwa sakamakon harin Iran
Sojojin Amurka bayan harin
Asali: Facebook

Babu Sojan Amurka da ya mutu ko ya samu rauni mai tsanani a lokacin da Iran ta kai harin rokoki masu linzami sansanin Ain Al Asad matsayin ramuwar gayya kan kisan Janar Qassem Soleimani da Amurka tayi ranar 3 ga Junairu, 2020.

Ramuwar gayyan ya kwantar da kuran rikicin yayinda dukkan bangarorin biyu basu kara kaiwa juna hari ba amma karuwar ciwon kwakwalwa da Sojin Amurka ke fama dashi yanzu na iya kara tayar da hankalin gwamnatin Trumo tayi tunanin sake kai hari.

A baya, shugaban kasar Amurka , Donald Trump, ya yi kokarin boye ciwon kwakwalwan da Sojin kasar suka samu sakamakon harin kuma ya gamu soke-soke daga wajen yan majalisar kasar da kungiyar tsaffin Sojojin Amurka.

A baya, Kakakin Pentagon, Jonathan Hoffman, ya bayyanawa manema labarai cewa: "Jimillar Sojoji 34 da aka gwada suna fama da rauni a kwakwalwa."

"Zasu cigaba da jinya a nan Amurka, ko a Walter Reed (Asibitin Sojojin dake kusa da Washington) ko a barikinsu."

Hakazalika, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa babu sojan Amurkan da aka rasa a harin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka ranar 7-8 na Junairu.

An fara rikici ne tsakanin Amurka da Iran ranar da Kasar Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatan hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel