Ashsha! Yan bindiga sun bindige mutane 2 har lahira a jahar Kaduna

Ashsha! Yan bindiga sun bindige mutane 2 har lahira a jahar Kaduna

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai wani samame da ake tunani kamar harin ramuwa ce biyo bayan ta’adin da dakarun rundunar Yansandan Najeriya suka yi musu a makon data gabata inda suka kashe sama da yan bindiga 250 a jahar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun kai wannan samame ne a ranar asabar 8 ga watan Feburairu a kauyen Gindin Dutse dake kusa da dajin Maidaro inda suka afka ma jama’an kauyen ta ko ina tare da bude musu wuta irin na mai kan uwa da wabi.

KU KARANTA: Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka

Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa shigarsu kauyen ke da wuya suka shiga harbin mai kan uwa da wabi, inda suka kashe mutane biyu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

“Ina cikin gonata a lokacin da wasu mazauna kauyen suka sameni suna fada min cewa yan bindiga fa sun shiga kauyen Gindin Dutse, kuma har sun kashe mutane biyu, kuma sun jikkata mutane biyu.” Inji shi.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo don jin ta bakinsa game da lamarin, sai ya bayyana cewa yana bukatar karin lokaci domin ya binciko.

A hannun guda kuma, fadar shugaban kasar Najeriya ta yi fatali da bayanan da kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Arewa Elders Forum fitar game da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta bayyana kungiyar a matsayin kungiyar mutum guda.

Kungiyar ta bakin shugabanta, Farfesa Ango Abdullahi ta bayyana cewa: “Talauci da matsalar tsaro sun kara ta’zzara a yankin Arewacin Najeriya a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

A wani labari kuma, Shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da rundunar Sojan kasa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa a yanzu dakarun rundunar Sojan kasa suna bin mayakan yan ta’addan Boko Haram har zuwa sansanoninsu domin gamawa dasu.

Ndume ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar asabar, inda yace Sojojin sun samu kwarin gwiwa ne biyo bayan umarnin da rundunar Sojan kasa ta bayar na su dinga kaddamar da hare hare a kan yan ta’addan ba sai sun jirasu ba.

Ndume yace a yan kwanakin da suka gabata ma Sojoji sun mayar da biki a kan wasu yan ta’adda a Kalla dake kusa da Dabua, inda suka yi ma yan ta’addan rakiyar Kura har zuwa sansanoninsu, inda suka lalatasu gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel