Maina zai cigaba da zama a Kurkuku, ya gaza cika sharrudan beli

Maina zai cigaba da zama a Kurkuku, ya gaza cika sharrudan beli

Lauyan Abdulrasheed Maina, Afam Osigwe, ya bayyana cewa Sanatocin majalisar dattawa sun ki tsaya masa domin cikka sharrudan belin da kotu ta gindaya masa.

Osigwe ya bayyana hakan a babban kotun tarayya dake Abuja ranar Alhamis, 6 ga watan Febraoru, 2020.

Yayinda aka dawo zaman kotu, Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya tambayi lauyan Maina shin ya samu cika sharrudan belinsa kuwa.

Lauyan, Osigwe, yace: "Abin da takaici, Sanatoci na kin tsayawa Maina."

Yace sun kokarin duba wasu hanyoyi daban na ganin yadda za'a cika sharrudan belin.

Maina zai cigaba da zama a Kurkuku, ya gaza cika sharrudan beli
Maina zai cigaba da zama a Kurkuku, ya gaza cika sharrudan beli
Asali: UGC

A ranar 29 ga Junairu, 2020 Babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Talata ta rage ka'idojin belin tsohon shugaban kwmaitin gyara harkan fansho, AbdulRashid Maina, daga bilyan daya zuwa milyan dari biyar.

Hakazalika Alkalin ya bukaci Maina ya gabatar da mai tsaya masa guda daya.

A ranar 13 ga Junairu, Maina ya bayyanawa kotu cewa har yanzu ya gaza cika sharruda masu tsaurin gaske da kotun ta kakaba masa na beli a watan Nuwamba.

A ranar Talata, 28 ga Junairu, Alkali mai shari'a, Okon Abang, yace: "Bisa ga hujjojin da aka gabatar gaban kotun, bai kamata in amsa bukatarsa (Maina) ba amma tun ranar da muka dage karar, ya natsu yanzu sabanin yadda yakeyi da farko."

"Zan ji tausayinsa in rage sharrudan."

"Ya biya kudin belin N500 miliyan, ya gabatar da mai tsaya masa kuma wajibi ne ya zama Sanata, wanda zai rika rakoshi kotu kullum."

Alkalin yace wajibi ne Sanatan ya mallaki dukiya a daya daga cikin wadannan unguwannin a birnin tarayya: Kamtape, Central Business District, Wuse 2, Maitama da Asokoro.

Ana zargin AbdulRashida Maina da laifin karkata kudi bilyan 100 na kudin fanshon al'umma.

Rundunar tsaro na DSS ce ta kama Maina da dansa a wani otel a Abuja sannan ta mikashi ga huumar EFCC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel