Mutum 3 sun hallaka, 179 sun jikkata yayinda jirgin saman yayi kaca-kaca a Turkiyya

Mutum 3 sun hallaka, 179 sun jikkata yayinda jirgin saman yayi kaca-kaca a Turkiyya

Lissafin yau Alhamis ya nuna cewa Fasinjoji uku ne suka hallaka kuma 179 sun jikkata a hadarin jirgin saman Pegasus da ya kauce kan titi yayin sauka a filin jirgin saman Istanbul a ranar Laraba, 5 ga watan Febrairu, 2020.

Jirgin ya rabe gida uku kuma ya fara kamawa da wuta kafin jami'an kwana-kwana suka kashe wutar.

Jirgin ya taso ne daga birnin Izmir domin zuwa filin jirgin saman Sabiha Gokcen kuma yanayin sararin samaniya babu kyau.

Mutum 3 sun hallaka, 179 sun jikkata yayinda jirgin saman yayi kaca-kaca a Turkiyya
Mutum 3 sun hallaka, 179 sun jikkata yayinda jirgin saman yayi kaca-kaca a Turkiyya
Asali: Facebook

Ministan Sufuri Mehmet Cahit Turhan yace babu wanda ya mutu, kuma yawancin fasinjojin sun sauka fita daga cikin jirgin da kansu.

"Wasu fasinjoji sun fita daga jirgin da kansu yayinda wasu ke turke ciki kuma ma'aikatanmu na kokarin fito da su." Yace

A jiya da abin ya faru, Gwamnan jihar Ali Yerlikaya yace: "A yanzu, mutane 120 suka jikkata kuma an kaisu asibiti... dukkansu na nan lafiya illa mutum daya zuwa biyu."

Allah ya kiyaye "da abin ya fi haka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel