Coronavirus: Kawo yanzu, mutane 24,500 sun kamu, 490 sun mutu, ta bulla kasashe 28, kalli jerin

Coronavirus: Kawo yanzu, mutane 24,500 sun kamu, 490 sun mutu, ta bulla kasashe 28, kalli jerin

Akalla mutane 490 sun mutu kawo yanzu a sakamakon cutar coronavirus da ta barke a kasar Sin. Wannan cuta ta fito ne a Yankin Wuhan, kafin cutar ta fara zagaya Duniya.

Kawo yanzu akwai mutane 24,500 da su ka kamu da wannan cuta a fadin Duniya. Ga jerin kasashe 28 da cutar ta bulla yanzu:

1. Sin - 20,438

2. Australiya - 14

3. Belguim - 1

4. Cambodia - 1

5. Canada - 4

6. Finland - 1

7. Faransa - 6

8. Jamus - 12

9. Hong Kong - 21

10. Indiya - 3

11. Italy - 2

12. Japan - 33

13. Macau - 10

14. Malaysiya - 12

15. Nepal - 1

16. Phillipines - 3

17. Rasha - 2

18. Singapore - 28

19. Koriya ta kudu - 19

20. Spain - 1

21. Sri Lanka - 1

22. Sweden - 1

23. Taiwan - 11

24. Vietman - 10

25. Thailand - 25

26. UAE (Dubai) - 5

27. Birtaniya - 2

28. Amurka - 11

Coronavirus: Kawo yanzu, mutane 24,500 sun kamu, 490 sun mutu, ta bulla kasashe 28, kalli jerin
Coronavirus
Asali: Twitter

A baya, Mun tsakuro bayanai daga gidan Aljazeera game da wannan mummunan cuta.

1. Mecece coronavirus?

Coronovirus ta na cikin dangin cututtuka irin su MERS da SARS da ke kawo matsalar numfashi. Cutar ta saba addabar dabbobi kafin yanzu ta bayyana jikin mutum.

2. Alamun cutar

Alamomin kamuwa da wannan cuta sun hada da:

1. Samun matsalar numfashi

2. Tari

3. Zazzabi

4. Gajeren numfashi

Wannan cuta ta na iya kai ga haifan ciwon pneumonia na sanyi da kuma matsalar koda da taba huhu. A karshe ta na iya kai ga cutar ajali.

Wannan cuta ba za ta yi irin ta’adin da SARS ta yi a 2002 ba inda mutane 800 su ka mutu. Masana kuma su na ganin ba za ta kai MERS illa ba.

3. Maganin cutar?

Kawo yanzu ba a kirkiro maganin da zai iya warkar da wannan cuta ba. Abin da ake yi shi ne kokarin ganin an hana cutar zagaya Duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel