Da duminsa: Yan ta'addan Ansaru sun budewa jirgin Yan sanda wuta, an kashe 250 cikinsu

Da duminsa: Yan ta'addan Ansaru sun budewa jirgin Yan sanda wuta, an kashe 250 cikinsu

Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da artabun da tayi da yan ta'addan Ansaru inda ta samu nasarar hallaka yan ta'addan 250 a jihar Kaduna.

Kakakin hukumar, Sunday Mba, ya ce yan sanda sunyi mumunan artabu da yan ta'addan da tsawon awanni da yawa a dajin Kuduru, karamar hukumar Birnin-Gwari, jihar Kaduna.

DCP Sunday Mba ya ce an kashe manyan yan ta'adda kungiyar Ansaru 250.

Kungiyar ta kasance mai addaban al'ummar jihar Kaduna ta hanyar garkuwa da mutane, fashi da makami, da barandanci a Arewacin Najeriya.

Sunday Mba ya bayyana cewa babu dan sanda da aka rasa amma wasu sun samu raunuka.

Yace: "Babu wanda aka rasa kuma babu hukumar tsaron da ta taba irin wannan nasarar. Wannan babban hari ne da ba'a taba tsammani ba."

Da duminsa: Yan ta'addan Ansaru sun budewa jirgin Yan sanda wuta, an kashe 250 cikinsu
Da duminsa: Yan ta'addan Ansaru sun budewa jirgin Yan sanda wuta, an kashe 250 cikinsu
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa Kungiyar yan ta'adda a Sudan, Jama'atu Ansarul Muslimeen, ta dau alhakin harin da aka kaiwa mai martaba sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Wannan alama ne na kungiyar Ansaru na kokarin dawowa bayan murkusheta tun shekarar 2012.

Harin karshe da yan ta'addan Ansaru suka kai shine garkuwa da turawa bakwai a kamfanin Setraco a jihar Kano a watan Febrairu 2013.

Bulama ya ce yan kungiyar sun dau alhakin harin ne a tashar yada labaran Al-Qa'ida, Thabat.

Wannan shine karo na farko tun shekarar 2013 da zasu dau alhakin kai wani hari.

Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da 100 lokacin da yan bindiga suka budewa motoci wuta a babbar titin Kaduna zuwa Zariya ranar 14 ga watan Junairu, 2020.

Hukumar yan sandan jihar, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa yan bindigan sanye da kayan Sojoji sun kai harin ne misalin karfe 11 na dare.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya ce mutane shida kadai aka kashe kuma biyar sun jikkata. Ya tabbatar da cewa an yi awon da wasu amma bai bayyana adadinsu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel