Coronavirus: Cikin kwanaki 10, an kammala ginin katafaren asibiti a China (Hotuna)

Coronavirus: Cikin kwanaki 10, an kammala ginin katafaren asibiti a China (Hotuna)

Maimata irin abinda akayi lokacin cutar SARS a 2003, gwamnatin jihar Wuhan a kasar Sin ta kaddamar da ginin asibitoci biyu Leishenshan da Huoshenshan a ranar 23 ga watan Junairu, 2020.

Cikin kwanaki 10, gwamnatin ta kammala ginin katafaren asibiti mai gado 1000 domin yakan cutar Coronavirus da ya bulla a garin Wuhan kuma ya yadi a akalla kasashen duniya 25 yanzu.

A ranar Lahadi, 2 ga Febrairu, an kammala ginin asibitin Huoshenshan kuma zau Litinin, 3 ga Febrairu, 2020.

Farawa da iyawa, an tura likitocin 1,400 daga hukumar Soji domin jinyar marasa lafiya a Asibitin yau.

Coronavirus: Cikin kwanaki 10, an kammala ginin katafaren asibiti a China (Hotuna)
Coronavirus: Cikin kwanaki 10, an kammala ginin katafaren asibiti a China (Hotuna)
Asali: UGC

Coronavirus: Cikin kwanaki 10, an kammala ginin katafaren asibiti a China (Hotuna)
Coronavirus: Cikin kwanaki 10, an kammala ginin katafaren asibiti a China (Hotuna)
Asali: Facebook

Legit.ng ta tsakuro bayanai daga gidan Aljazira game da wannan mummunan cuta.

1. Mecece coronavirus?

Coronovirus ta na cikin dangin cututtuka irin su MERS da SARS da ke kawo matsalar numfashi. Cutar ta saba addabar dabbobi kafin yanzu ta bayyana jikin mutum.

2. Alamun cutar

Alamomin kamuwa da wannan cuta sun hada da:

1. Samun matsalar numfashi

2. Tari

3. Zazzabi

4. Gajeren numfashi

Wannan cuta ta na iya kai ga haifan ciwon pneumonia na sanyi da kuma matsalar koda da taba huhu. A karshe ta na iya kai ga cutar ajali.

Wannan cuta ba za ta yi irin ta’adin da SARS ta yi a 2002 ba inda mutane 800 su ka mutu. Masana kuma su na ganin ba za ta kai MERS illa ba.

3. Ina ake fama da cutar?

Yanzu wannan cuta ta yi kamari ne a Sin. Bayan nan ta fara shiga kasashe kamar Thailand, Koriya ta Kudu, Taiwan, Jafan da Amurka.

4. Maganin cutar?

Kawo yanzu ba a kirkiro maganin da zai iya warkar da wannan cuta ba. Abin da ake yi shi ne kokarin ganin an hana cutar zagaya Duniya.

5. Daga ina cutar ta fito?

Kwayar cutar Coronavirus ta fara barkewa ne a kasar Sin, amma yanzu haka ana bincike domin gano ainihin daga inda cutar ta fara fitowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel