Manoma 2 sun gamu da ajalinsu a gonakansu a hannun yan bindiga dadi

Manoma 2 sun gamu da ajalinsu a gonakansu a hannun yan bindiga dadi

Wasu manoma guda biyu sun gamu da ajalinsu a hannun miyagu yan bindiga dadi yayin da suke tsaka da aikace aikacen gona a cikin gonakansu a kauyen Dapye daga cikin karamar hukumar Wukari ta jahar Taraba.

TheCables ta ruwaito shugaban karamar hukumar Wukari, Adigrace Daniel ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru inda ya bayyana sunayen manoman da aka kashe kamar haka; Siman Bala da Timothy Awe.

KU KARANTA: Shuwagabannin PDP sun gudanar da zanga zanga a ofishin Amurka da Birtaniya

Ciyaman Daniel yace yan bindigan sun kashe manoman ne yayin da suke gudanar da aiki a gonakansu, sai dai yace wasu tawagar jami’an tsaro sun isa inda lamarin ya auku kuma sun tattara bayanai game da yan bindigan, amma basu tarar da kowa a wurin ba sai gawarwakin manoman.

Haka zalika jami’in hulda da jama’a na rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Taraba, David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace tuni Yansanda suka fara kokarin bin sawun yan bindigan tare da kamasu.

A yan kwanakin nan dai an samu rahotanni tashe tashen hankula da kashe kashe a karamar hukumar Wukari, inda kabilun Jukuna da Tibi suke kai ma junansu hare hare ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sanye da kayan Sojoji da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun bude ma wasu babbar motar Luxurious wuta a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja inda suka ji ma mutane hudu rauni.

Wannan lamari ya faru ne a gab da kauyen Gada-Biyu dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu, inda yan bindigan suka bude ma motar kamfanin Chisco wuta mai lamba AGL 11 XL.

Direban babbar motar mai suna Madu Francis ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:47 na yamma a lokacin da yake gangarawa Gada-Biyu, kwatsam sai ganin wasu mutane sanye da kakin Sojojo sun fito daga cikin daji sun bude musu wuta da bindigu.

Madu ya kara da cewa adadin yan bindigan yah aura 30, don haka wutan da suka bude ma motar tare da fasinjojinta ya yi karfi sosai, wanda hakan yasa da dama daga cikinsu suka samu rauni a sanadiyyar harbe harben.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel