An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami

An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arziki da ya dogara da fasahar zamani, Dr Isa Ali Pantami ya sanar da cewa tabbatar da tsarin Integrated Payroll and Personel Information System (IPPIS) ya sa an bankado ma'aikatan bogi har 6,000 a gwamnatin tarayya.

Pantami ya bayyana hakan ne a yayin bikin yaye dalibai karo na 29 a jami'ar fasaha da ke Minna a jihar Neja, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ministan, wanda ya bayyana manufar gwamnatin tarayya na hana ci gaban rashawa a Najeriya, ya kara bayyana cewa gwamnatin tarayya ta adana naira biliyan 24 tun bayan da ta tabbatar da asusun bai daya (TSA) a kasar nan.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta kirkiro da tsarin IPPIS da TSA don kawo karshen rashawa a kasar nan.

An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami
An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: 'Yan Najeriya da ke China ba su son dawowa gida - Lai Mohammed

A wani rahoton da Legit.ng ta ruwaito cewa, ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa 'yan Najeriya mazauna birnin Wuhan a kasar China da aka samun bullar Coronavirus sun bayyana cewa ba su da niyyar dawowa gida Najeriya.

Da ya ke jawabi yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma'a, 31 ga watan Janairu, Lai Mohammed ya ce tuni sun tuntubi 'yan Najeriya 16 da ke zaune a birnin Wuhan.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta iya hana 'yan Najeriya tafiya kasar China ba duk da bullar anobar cutar da Coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel