'Yan bindiga sun kai wa fasinjojin jirgin kasa hari a Kaduna

'Yan bindiga sun kai wa fasinjojin jirgin kasa hari a Kaduna

'Yan bindiga sun kai wa matifiya hari a tashan jirgin kasa na Rigasa a Kaduna a ranar Juma'a 24 ga watan Janairu.

Matafiyan suna shirin shiga motocin da za su kai su gidajensu bayan sun iso Kaduna daga Abuja ne kwatsam sai 'yan bindigan suka far musu.

Duk da cewa a tabbatar ko 'yan bindigan sun sace wasu daga cikin fasinjojin a halin yanzu ba, wata majiya daga hukumomin tsaro da ta zanta da The Cable ta ce matifyan sun bar motocinsu a bakin titi sun tsere cikin daji yayin harin.

'Yan bindiga sun bude wa fasinjojin jirgin kasa wuta a Kaduna
'Yan bindiga sun bude wa fasinjojin jirgin kasa wuta a Kaduna
Asali: UGC

Majiyar tsaron ta ce; "Lokacin da jirgin kasar da ya taso Abuja karfe 6.30 na yamma ya iso Kaduna misalin karfe 8 na dare. Wasu daga cikin fasinjojin sun karasa gidajensu amma wadanda suka yi kokarin shiga gari ta hanyar Rigasa zuwa Airport sun gama da sharrin wasu 'yan bindiga."

DUBA WANNAN: Lafiya jari: Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam

Wannan hari na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu 'yan bindiga sun kai wa tawagar Sarkin Potiskum na jihar Yobe, Alhaji Umaru Bubaram hari a hanyar Kaduna.

'Yan bindigan sun kashe wasu daga cikin hadimansa tare da yin garkuwa da guda daya daga cikinsu.

Sarkin na Potiskum ya bayar da labarin yadda ya sha da kyar ya kuma yi tafiya na sa'o'i a cikin dajin domin ya tsira daga harin na yan bindigan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel