Sakamakon harin Iran, Sojojin Amurka 34 sun samu rauni a kwakwalwa - Pentagon

Sakamakon harin Iran, Sojojin Amurka 34 sun samu rauni a kwakwalwa - Pentagon

Kimanin Sojojin Amurka dozin uku ne suka samu rauni a kwalkwalwa sakamakon harin ramuwar gayya da kasar Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraqi, hedkwatar Sojin Amurka, Pentagon ta bayyana ranar Juma'a.

Kakakin Pentagon, Jonathan Hoffman, ya bayyanawa manema labarai cewa: "Jimillar Sojoji 34 da aka gwada suna fama da rauni a kwakwalwa."

Da farko, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa babu sojan Amurkan da aka rasa a harin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka ranar 7-8 na Junairu.

Daga baya hukumomi suka bayyana cewa Sojin Amurka 11 sun jikkata.

Amma a yau, Hoffman ya ce bayan harin, an kai Sojoji 17 kasar Jamus domin jinya kuma takwas cikinsu sun dawo Amurka ranar Juma'a.

Yace: "Zasu cigaba da jinya a nan Amurka, ko a Walter Reed (Asibitin Sojojin dake kusa da Washington) ko a barikinsu."

Sauran taran da 9 da ke Jamus "na cigaba da jinya a can"

Sauran 17 da suka samu rauni tuni sun samu sauki kuma sun koma aiki a Iraqi.

Sakamakon harin Iran, Sojojin Amurka 34 sun samu rauni a kwakwalwa - Pentagon
rOKOKIN DA iRAN TA HARBA
Asali: Facebook

DUBA NAN: Sai ka yi nadama bayan mulkinka - Kwankwaso ya yiwa Ganduje raddi

An fara rikici ne tsakanin Amurka da Iran ranar da Kasar Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatan hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng