Cutar Corona Virus: Kasar Sin na shirin gina sabon asibiti kwanaki 10 domin jinyar wadanda suka kamu

Cutar Corona Virus: Kasar Sin na shirin gina sabon asibiti kwanaki 10 domin jinyar wadanda suka kamu

Kasar Sin ta fara shirin gina sabon asibitin da za'a kammala cikin kwanaki goma kacal domin jinyar marasa lafiyan da suka kamu da cutar Corona Virus da ta addabi kasar inda daruruwan mutane sun kamu, Xinhua ta ruwaito.

Za'a fara gina asibitin a garin Wuhan kuma ana sa ran fara amfani da sabon asibitin daga ranar 3 ga watan Febrairu dubi ga yadda yawan marasa lafiya ke karuwa bayan kimanin mutane 26 sun hallaka.

A yanzu haka, an hana mutane shiga da fice daga garin Wuhan. Hukumomin kasar sun kulle tashohin mota, jiragen sama, jiragen kasa da sauransu.

An ga kayayyakin aiki a wajen da ake gina asibitin da ake sa ran zai dauki masu jinya 1000 a lokaci guda.

An kaddamar da ginin ne bayan mutane sun cika asibitocin da ke garin inda kimanin mutane 830 suka kamu da cutar Corona Virus.

Tashar yada labarai Xinhua ta ce ana kyautata zaton gina sabon asibitin zai taimaka wajen samun isasshen wuri domin kula da marasa lafiya.

A shekarar 2003, kasar Sin ta gina irin wannan asibitin da birnin tarayyar Beijing lokacin da annobar cutar SARS ya hallaka mutane 349 a birni da kuma 299 a Hong-Kong.

Legit.ng ta tsakuro bayanai daga gidan Aljazira game da wannan mummunan cuta.

1. Mecece coronavirus?

Coronovirus ta na cikin dangin cututtuka irin su MERS da SARS da ke kawo matsalar numfashi. Cutar ta saba addabar dabbobi kafin yanzu ta bayyana jikin mutum.

2. Alamun cutar

Alamomin kamuwa da wannan cuta sun hada da:

1. Samun matsalar numfashi

2. Tari

3. Zazzabi

4. Gajeren numfashi

Wannan cuta ta na iya kai ga haifan ciwon pneumonia na sanyi da kuma matsalar koda da taba huhu. A karshe ta na iya kai ga cutar ajali.

Wannan cuta ba za ta yi irin ta’adin da SARS ta yi a 2002 ba inda mutane 800 su ka mutu. Masana kuma su na ganin ba za ta kai MERS illa ba.

3. Ina ake fama da cutar?

Yanzu wannan cuta ta yi kamari ne a Sin. Bayan nan ta fara shiga kasashe kamar Thailand, Koriya ta Kudu, Taiwan, Jafan da Amurka.

4. Maganin cutar?

Kawo yanzu ba a kirkiro maganin da zai iya warkar da wannan cuta ba. Abin da ake yi shi ne kokarin ganin an hana cutar zagaya Duniya.

5. Daga ina cutar ta fito?

Kwayar cutar Coronavirus ta fara barkewa ne a kasar Sin, amma yanzu haka ana bincike domin gano ainihin daga inda cutar ta fara fitowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel