Lafiya jari: Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam

Lafiya jari: Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam

Binciken kimiyya ya bayyana cewa bayan karin dandano da karas yake karawa abinci yana kuma dauke da sinadarai masu yawa da suka hada da antioxidants, beta-carotene, alpha-carotene, lutein, potassium, vitamin C, vitamin A, fibre da Carotenoids.

Lafiya jari: Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam
Lafiya jari: Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam
Asali: Twitter

A sakamakon wannan sunadarai da karas ya kunsa, ga cututtuka takwas da yake kawarwa:

1. Taimakawa wurin kiyaye kamuwa da ciwon daji (kansa)

Karas na dauke da sinadarai masu yawa da masana ke kira 'Phytochemicals' da ke yaki da cutan daji. Wasu daga cikin sinadaren sun hada da beta-carotene da sauransu. Wadannan sinadaren na karfafa garkuwar jiki. Masana sun kuma gano karas na iya maganin Leukemia da kare yiwuwar kamuwa da ciwon daji na baki.

2. Inganta Lafiyar Ido

Sinadarin Vitamin A yana taimakawa idanu su rika gani tangaran kuma karas na dauke da Vitamin A masu yawa. Idan mutum ya rasa Vitamin A na lokaci mai tsawo, yana iya fara samun da ganinsa.

3. Gyara fatan jiki

Karas na dauke da sinadarai masu yawa da ake kira 'carotenoids'. Binciken kimiyya ya nuna cewa 'ya'yan itatuwa da ganye suna dauke da sinadarai na ke inganta lafiyar mutum ya kuma haskaka fatarsa ya. Sai dai cin karas din fiye da kima yana iya haifar da matsala mai suna 'carotenosis' da ke saka fatar mutum tayi haske da yawa.

4. Bugun Zuciya

Wani sabon bincike da masana kimiyya suka gudanar ya nuna cewa ruwan da aka tatsa daga karas na rage hawan jini da kashe 5 cikin 100. Sinadaren da ke cikin karas da suka hada da fibre, potassium, nitrates da Vitamin C ne ke taimkawa wurin wannan.

5. Taimakawa masu ciwon suga

Cin abinci mai inganta lafiya yana taimakawa wurin rage kiba da kuma hana kamuwa da ciwon suga nau'i na biyu. Bincike ya nuna cewa Vitamin A na kare afkuwa da kamuwa da ciwon suga kuma tunda karas na kunshe da sinadarin sosai yana iya taimakawa.

6. Karfafa kashi

Vitamin A yana taka muhimmiyar rawa wurin gyara kashin dan adam. Beta-carotene da karas ke dauke da shi yana kare kwayoyin hallita daga cututuka kuma yana taimakawa inganta lafiyar kashi.

7. Cututtukan baki da hakori

Danyen karas yana taimakawa wurin kawar da kwayoyin cuta daga hakora kuma ya washe numfashin mutum. Fibre da karas ke dauke da shi yana kara adadin yawu a bakin mutum da ka iya taimakawa ya rage adadin citric acid a malic acid da ke bakin dan adam.

DUBA WANNAN: Rashawa: Ba zan sassauta wa Abubakar ba - Gwamnan Bauchi

8. Inganta lafiyar hanta

Karas na dauke da glutathione, wani muhimmin sinadari da ke kawar da ababen da ke cutar da hanta. Karas har ila yau na dayke da beta carotene da Vitamin A da ke inganta aikin hantar dan adam da kare ta daga cututtuka.

9. Kara karfin garkuwar jiki

Vitamin A yana taimakawa wurin aiwatar da wasu ayyuka a jiki tare da kare cututtuka. Hakan na yiwuwa ne saboda yana inganta garkuwar jikin mutum. Karas kuma na dauke da Vitamin C da shima ke karfafa garkuwar jiki.

10. Rage cholesterol (kitse)

Cin karas na rage adadin cholesteral da ke shiga jikin adam da kuma kara sinadarai masu yaki da cututtuka. Hakan na inganta lafiyar zuciya. Danyen karas na kunshe da lectin da ke taimakawa wurin rage cholesteral.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel