Yanzu-yanzu: An tashi, Ganduje ya lallasa Abba Gida-gida a kotun koli

Yanzu-yanzu: An tashi, Ganduje ya lallasa Abba Gida-gida a kotun koli

Labari kai tsaye daga kotun kolin Najeriya dake Abuja da nuna cewa Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi karar Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje matsayin zababben gwamnan jihar Kano a zaben Maris, 2019.

Alkalan kotun gaba daya karkashin jagorancin Jastis Sylvester Ngwuta sun yi ittifakin cewa karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar bata da karfi.

Dan takarar Peoples Democratic Party (PDP), Abba Kabir Yusuf, ya shigar da kara ne kan karashen zaben Kanon da akayi ranar 23 ga watan Maris bayan shi ke kan gaba a zaben da akayi ranar 9 ga Maris.

Abba Kabir Yusuf da jam'iyyarsa sun bukaci kotun tayi watsi da zaben ranar 23 ga Maris kuma an alantashi a matsayin zababben gwamna tun da shi ke da rinjaye.

Abba-Yusuf ya ce duba da cewa shine ya samu kuri'u mafi rinjaye, shine dan takarar da ya cika tanadin sashi na 179 na dokar zabe.

Da ya ke jawabi kan daukaka kararsa, Adegboyega Awomolo (SAN), ya bukaci kotun kolin da ajiye hukuncin da kananan kotuna da - kotun zabe da kotun daukaka kara su kari a kan shari'ar na tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Awomolo ya ce baturen zabe na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a Kano ya sanar da sakamakon zaben ranar 9 ga watan Maris 2019 na kananan hukumomi 44 a jihar Kano kuma ya bayar da fom EC8D da ke dauke da takaitaccen kuri'un da aka sanar a rumfunan zabe 207.

Ya ce kotun koli a wasu shari'ar da bayyana cewa saba doka ne baturen zabe ya soke sakamakon zaben kananan hukumomi bayan ya riga ya sanar.

Ya ce, "Bayyana cewa zabe bai kammalu ba (inconclusive) bayan soke sakamakon rumfunan zabe 207 lamari ne da ya fi karfin ikon baturen zabe."

Sai dai Ahmed Raji (SAN), Alex Izinyon (SAN) da Offiong Offiong (SAN) da ke wakiltan INEC, APC da Gwamna Ganduje kamar yadda aka jera sun bukaci kotun kolin ta yi watsi da daukaka karar ta Kabiru Yusuf da PDP.

Raji ya ce babu wata hujja da ke nuna baturen zaben ya soke sakamakon zabe amma abinda ya ke a hukumance shine baturen zaben ya kasa tattara sakamakon zaben a ranar.

Ya ce, "Ina kira ga mai daraja ya yi watsi da wannan daukaka karar ya kuma tabbatar da hukuncin da kananan kotunan suka bayan a baya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel