Shari'ar kotun koli: Har yanzu a kidime nike - Emeka Ihedioha

Shari'ar kotun koli: Har yanzu a kidime nike - Emeka Ihedioha

Tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Emeka Ihedioha, wanda kotun koli ta fitittika ranar Talata matsayin gwamnan jihar Imo ya bayyana cewa har yanzu a kidime yake.

Ihedioha ya ce sakamakon kotun bai zai sa ya fidda rai daga demokradiyyan Najeriya ba.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a gidansa dake Abuja lokacin mambobin kwamitin gudanarwan PDP suka kawo masa ziyarar jaje bisa ibtila'in da ya afka masa.

Ya ce wannan lokaci ne da ya kamata ya zauna yayi nazari kuma duk wanda yayi farin cikin wannan faduwa da yayi ya jahilci demokradiyya.

"Yadda abin ya ya kidimar daku haka muka kidime. Bamu taba tunanin haka ba. Dukkan masu sharhi kan lamuran shari'a basu taba tunanin haka. Saboda haka har yanzu abin mamaki yake bamu." Yace

A ranar Talata, Kotun koli a ranar Litnin ta fitittiki Emeka Ihedioha na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) matsayin gwamnan jihar Imo.

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

Saboda haka, ta yi watsi da sanarwan INEC na baiwa Emeka Ihedioha nasara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel