Yanzu-yanzu: Buhari zai tafi London gobe Juma'a

Yanzu-yanzu: Buhari zai tafi London gobe Juma'a

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Juma'a ya tafi birnin London domin hallartan taron saka hannun jari tsakin Afirka da Ingila da za a gudanar a ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2020.

A cewar masu shirya taron, Farai ministan Burtaniya, Boris Johnson ne ake sa ran zai zama mai masaukin baki inda ake sa ran shugabanin Afirka da shugabanin kamfanoni na kasa da kasa su hallarci taron.

Sanarwan da kakakin shugaban kasa Femi Adesina ya fitar ya ce ana sa ran taron zai "kula kawance da zai samar da ayyuka da saka hannun jari" da zai amfani mutanen Afirka da Ingila.

Tawagar Najeriya da za ta hallarci taron za ta nuna wa duniya irin sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta yi da hanyar kirkiran sabbin dokoki da za su inganta kasuwanci a kasar.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta ce za ta binciki gwamnonin da suka yi ruf-da-ciki da kudaden kananan hukumomi

Mr Adesina ya ce ana kuma sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai gana da shugaban kasashen da Ingila ta raina, Yarima Charles a Glasgow a Scotland.

Wannan shine karo na farko da shugaban kasar zai fita kasan waje a 2020 kuma gwamnonin da za su masa rakiya sun hada da Yahaya Bello na jihar Kogi, Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe da Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Sauran wadanda za su tafi tare da shugaban kasar sun hada da Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Masana'antu, kasuwanci da saka jari, Otunba Niyi Adebayo, Ministan Kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed; Mai bawa shugaban kasa shawara a fanin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno (murabus) da shugaban NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo gida Najeriya a ranar Alhamis mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel