Cikakken bayani: Dalilin da yasa kotun koli ta baiwa APC nasara a Imo

Cikakken bayani: Dalilin da yasa kotun koli ta baiwa APC nasara a Imo

Kotun koli a ranar Litnin ta fitittiki Emeka Ihedioha na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) matsayin gwamnan jihar Imo.

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

Saboda haka, ta yi watsi da sanarwan INEC na baiwa Emeka Ihedioha nasara.

Hakazalika, kotun ta umurci hukumar INEC ta kwace shahadar nasarar zabe daga hannun Emeka Ihedioha kuma ta mikawa Hope Uzodinma na jam'iyyar APC.

A cewarta: "An zabge Kuri'un da Sanata Hope Uzodinma na APC ya samu a rumfunan zabe 388. Saboda haka mun bada umurnin dawo masa da kuri'un da ya samu a wadannan rumfuna 388 kuma hakan ya nuna cewa Emeka Ihedioha bai samu kuri'u mafi rinjaye ba."

"Mun yi watsi da sanar da shi matsayin zababben gwamnan jihar Imo."

"Bayan hakan, mun alanta mai kara (Hope Uzodinma) matsayin wanda ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben jihar Imo da ya gdana ranar 9 ga Maris , 2019."

"Mun alanta mai kara, Sanata Hope Uzodinma, matsayin zakaran zaben gwamnan jihar Imo da aka gudanar ranar 9 ga Maris, 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel