Yanzu-yanzu: An sake kai harin roka mai linzami sansanin Sojin Amurka

Yanzu-yanzu: An sake kai harin roka mai linzami sansanin Sojin Amurka

An kai mumunan harin rokoki sansanin sojin Balad da Sojin Amurka ke zaune a birnin Baghdada dake kasar Iraqi, jami'an tsaro sun tabbatar.

AFP ta ruwaito cewa tuni Sojojin Amurka sun arce daga sansanin kuma Sojin kasar Iraqi hudu suka jikkata a yanzu.

Wani jami'in dan sandan yankin Salah-Al-Din ya bayana cewa rokokin sun dira cikin sansanin Sojin saman.

Yace: "Sojojin Iraqi uku dake gadi sun jikkata sakamakon harin."

Kawo yanzu, babu wanda ya dau alhakin wannan hari yayinda ake kishin-kishin yaki tsakanin Amurka da Iran.

A makon da ya gabata, Iran ta harba rokoki masu linzami 20 sansanin Sojin Amurka dake Iraqi domin mayar da martani kan kisan babban kwamandan Iran, Qassem Soleimani, da Amurka tayi ranar Juma'a.

Sansanin Ayn Al Asad da Sansanin Erbil Asad ne aka harba manyan rokokin misalin karfe 5:30 na yammacin Talata kuma da alamun akalla sojojin Amurka 80 sun hallaka.

Amma Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu dan Amurkan da ya samu rauni a harin bama-bamai masu linzamin da Iran ta kai sansanin Sojin Amurka dake Iraqi.

Trump ya yi kira ga kasashen Turai, Rasha, Sin, Jamus da Ingila su fita daga yarjejeniyar nukiliyan da suka shiga a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel