Zuwan Hanan Buhari Bauchi daukan hoto a jirgin shugaban kasa ya jawo cece-kuce

Zuwan Hanan Buhari Bauchi daukan hoto a jirgin shugaban kasa ya jawo cece-kuce

A ranar Alhamis ne autar Buhari, Hanan Buhari tayi dirar mikiya a jihar Bauchi don halartar wani hawan daba na musamman a fadar sarkin Bauchi. Hanan ta isa jihar Bauchi ne a jirgin shugaban kasa.

Zuwan Hanan a jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani. Mutane da yawa sun kushe al'amarin domin anyi amfani da jirgin sama ne na sojin saman Najeriya don biyan bukatar ta.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Hanan Buhari kwararriyar mai daukar hoto ce wacce ta kammala digirinta a fannin daukar hoto daga wata jami'a a London. Hakazalika, Hanan ta fita ta sakamako na ajin farko a fannin da ta karanta na daukar hoton.

Kwararriyar mai daukar hoton ta sauka ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi a ranar Alhamis. Ta samu tarba ne daga uwargidan gwamnan jihar Bauchi da sauran manyan jami'an gwamnatin jihar.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Yadda wani mutum ya yi ta lalata da karya daga bisani ya kashe ta

An gano cewa an shirya hawan daban ne don autar shugaban kasan ta samu damar daukar hawan, gine-ginen gargajiya da kuma sauran wuraren al'adu na jihar.

A matsayinta na kwararriya a fannin daukar hoton, Hanan zata hada hotunan ne don samun kundi guda na al'adu, hawa da gine-ginen masarautar jihar Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel