Banbancin gwamnatin Buhari da Boko Haram, tayar da bama-bamai - Matthew Kukah

Banbancin gwamnatin Buhari da Boko Haram, tayar da bama-bamai - Matthew Kukah

Babban faston katolikan jihar Sokoto, Matthew Kukah, ya ce banbancin dake tsakanin gwamnati da yan Boko Haram wajen kokarin Musuluntar da Najeriya shine Bam

A cewar PUNCH, Kukah ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda yake jawabi a wani taron Katolika a kasar Ingila.

Rahoton ya kawo cewa Matthew Kukah yana jawabi ne kan kisan mabiya addinin Kirista 10 da yan kungiyar tada kayar bayan ISWAP suka kashe ranar Kirismeti.

Faston ya tuhumci gwamnati da amfani da hanyoyi daban-daban domin cimma manufa daya na Musuluntar da Najeriya kaman Boko Haram.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta yi kasa a gwiwa wajen dakile yan Boko Haram kuma ta baiwa yan ta'addan damar cin karansu ba babbaka kamar yadda sukeyi yanzu.

"Banbanci daya da ke tsakanin gwamnati da Boko Haram shine Boko Haram na amfani da Bam."

"Suna amfani da akalan mulki wajen karfafa addinin Musulunci, wanda ke kara musu karfin tunanin cewa zasu cimma manufar hakan ta hanyar yaki."

""Yadda abubuwa suke yanzu a Najeriya, da alamun babu niyyar kawar da Boko Haram."

"Sun samar da abubuwan dake sanya Boko Haram yin abin da suka ga dama."

"Idan akwai kasan da dukkan matsayi Musulmi ake baiwa, toh ana nuna cewa addinin Musulunci ake kokarin karfafawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel