Sayen tsohon layin waya da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi ya jawo wa matashi daurin watanni

Sayen tsohon layin waya da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi ya jawo wa matashi daurin watanni

Jami'an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kama tare da tsare wani matashi, Anthony Okolie, sakamakon ya sayi wani layin waya na kamfanin sadarwa, MTN, da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi a baya.

Okolie ya sayi layin wayar ne tun a shekarar 2018, shekaru biyu kafin kamun da jami'an tsaro suka yi masa.

An kama shi ne ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, 2019.

Jami'an DSS sun yi awon gaba da Okolie zuwa Abuja kafin daga bisani ya shaki iskar 'yanci a watan Disamba, 2019.

Kokarin majiyarmu na jin ta bakin hukumar DSS a kan lamarin ya ci tura kasancewar kakakin hukumar, Peter Afunanya, bai amsa kira ko bayar da amsar sakon da aka aike masa ba a kan lamarin kafin wallafa wannan labari.

Sayen tsohon layin waya da diyar Buhari, Hanan, ta taba amfani da shi ya jawo wa matashi daurin watanni
Hanan Buhari
Asali: Twitter

Tope Akinyode, lauyan Okolie, ya ce hukumar DSS ta tsare matashin na tsawon makonni 15.

Akinyode, ya bayyana cewa kamfani ne ya sake dawo da layin wayar kasuwa bayan Hanan ta daina amfani da shi.

DUBA WANNAN: Darektan hukumar kwana - kwana ta Kano ya mutu

"Ya sayi layin waya ne bisa ka'ida ba tare da sanin waye ya yi amfani da shi ba a baya," a cewar Akinyode.

Lauyan ya kara da cewa an saba ka'ida wajen kama Okolie tare da tsare shi a kan layin da ya saya kuma aka bashi takardar shaidar cinikayya (Receipt).

Akinyode ya sanar da cewa Okolie zai shigar da karar da hukumar DSS da Hanan Buhari domin neman diyyar hakkinsa da aka take.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel