Bamu kara farashin wutan lantarki ba tukun - NERC ta yi amai ta lashe

Bamu kara farashin wutan lantarki ba tukun - NERC ta yi amai ta lashe

Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC ta yi amai ta lashe inda ta yi bayanin cewa ba ta kara farashin wutan lantarki ba tukun.

Jami'an hulda da jama'a na hukumar NERC, Usman Arabi, ya yi fashin baki kan lamarin a jawabin da ya daura a shafin yanar gizon hukumar ranar Lahadi.

Arabi yace: "An jawo hankalin NERC kan labarin da kafafan yada labarai ke yadawa na cewa an kara farashin wutan lantarki ."

"Hukumar na sanar da al'umma cewa babu karin farashin da akayi tukun."

Yan Najeriya sun yi ca kan gwamnatin tarayya yayinda hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC a ranar Asabar ta sanar da karin farashin wutan lantarkin fadin tarayya fari daga ranar 1 ga watan Junairu, 2020.

Hukumar ta umurci dukkan kamfanonin raba wutan lantarki 'Discos' tun ranar 31 ga Disamba, 2019 amma sai yau ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Shugaban hukumar, Joseph Mohmoh da kwamishanan bada lasisi, Dafe Akpenye, ne suka rattaba hannu kan umurnin.

Wadanda wannan kari kari ya shafa sune kamfanin raba wutan Abuja AEDC, Benin BEDC, Enugu EEDC, Eko EKDC, Ibadan IEDC, Ikeja , Jos , Kaduna KEDC , Kano KEDCO , Port Harcourt da Yola YEDC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel