Saratu Gidado ta zama jakadiyar tallafawa mabukata

Saratu Gidado ta zama jakadiyar tallafawa mabukata

Wata gidauniyar tallafawa mabukata mai suna 'World Wide Initiative for Community Development and Global Healthcare' ta nada fitacciyar jaruma Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso a matsayin jakadiyar bada gudunmawa ga mabukata a cikin birni da kauyuka.

A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar ta gudanar da taron ta na shekara a Kano, inda aka karrama fitattun mutane. Cikinsu kuwa har da Saratu Gidado.

Baya ga karrama Saratu da aka yi, sai aka naɗa ta a matsayin jakadiya domin tare da ita za a riƙa tafiya a matsayin ta na wadda aka san fuskar ta saboda ta riƙa wayar da kan jama'a dangane da ayyukan ƙungiyar.

A katuwar shaidar nadin da aka bata, wadda jagorar gidauniyar, Dakta Baraka Sani, ta rattaba hannu a kai, an nuna cewa za ta yi wannan aiki ne a tsawon shekara daya. Wato daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Disamba na 2020.

A yayin da wakilin mujallar fim yaji ta bakin fitacciyar jarumar dangane da wannan aikin da aka dora mata, ta bayyana cewa, "An nada ni jakadiya ne don na kasance wacce aka sani a fuskar duniya, domin haka zamuyi aiki tare dasu.

DUBA WANNAN: Sunaye: Ganduje ya nada sabbin hadimai 17

"Duk inda zasu je, idan ina da lokaci sai mu tafi tare da su don wayar da kan jama'a, musamman a yankunan karkara. Kasan bakuwar fuska na da wuyar sha'ani ga mutane. Zai yi wuya su karbi abin da aka je masu dashi ba tare da sun ga fuskar da suka sani ba. Amma idan sun ganni, zasu saurin aminta ko sauraron abinda aka je dashi.

"Amma ni an bani matsayin jakadiya ne a wannan kungiyar, don haka ina tare da su a wannan matsayin."

Ba wannan bane karo na farko da kungiyoyi ko kamfanoni suke daukar 'yan fim din Hausa a matsayin jakadun su domin tallata manufarsu ga jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel