Komai ta fanjama: An umarci Yansandan Najeriya su zama cikin shiri bayan kisan Janar Soleimani

Komai ta fanjama: An umarci Yansandan Najeriya su zama cikin shiri bayan kisan Janar Soleimani

A wani mataki na kan da garki, ko kuma kamar yadda masu iya magana kan ce, wai “rigakafi ya fi magani” Babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya umarci jami’an Yansandan Najeriya su zauna a cikin shiri ta yadda komai ta fanjama fanjam!

IG Adamu ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan kisan wani babban kwamandan yaki na kasar Iran da gwamnatin kasar Amurka ta kashe shi a makon da ta gabata, inda yace sun samu labarin akwai wasu dake shirin tayar da hankulan jama’a a Najeriya tare da yi ma gwamnatin Najeriya zagon kasa.

KU KARANTA: Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria

Da wannan ne IG Adamu ya umarci kwamishinonin Yansanda, da AIG na shiyya shiyya da su tabbata sun sanya idanu sosai domin tabbatar da tsaron dukiya da rayukan al’umma a duk fadin kasar nan.

Sanarwar wanda mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya, DCP Frank Mba ya fitar ta bayyana an umarci kwamandojin Yansanda su tabbata sun tura jami’ansu na fili da na boye zuwa wuraren da suka kamata don samar da isashshen tsaro.

Kaakakin Yansanda ya kara da cewa manufar wannan umarni shi ne tsaurara matakan tsaro domin kare rayukan jama’a, rayukan yan kasashen waje mazauna Najeriya, jakadun kasashen waje a Najeriya da ofisoshinsu, da kuma kadarorin gwamnati.

Daga karshe babban sufetan Yansanda ya baiwa yan Najeriya da sauran kasashen waje dake zaune a Najeriya tabbacin tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu, sa’annan ya gargadi duk wasu nufin tayar da zauni tsaye dasu kiyayi fitowa kan titunan Najeriya da ma kasar gaba daya.

A wani labarin kuma, tun bayan kisan Janar Soleimani, an cigaba da samun musayar yawu tsakanin gwamnatocin Amurka da na Iran, inda kowannensu ke barazanar kai ma dayar hari, yayin da Iran ke kumfar bakin kai ma Amurka ramuwar gayya, Amurka kuma kashedi take yi ma Iran.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel