Yan Hibah sun kama matasa 'yan 'luwadi' 15 yayin bikin murnar kammala Jami'a a Kano

Yan Hibah sun kama matasa 'yan 'luwadi' 15 yayin bikin murnar kammala Jami'a a Kano

Hukumar tabbatar da biyayya ga dokokin addinin Musulunci wacce aka fi sani da "HISBAH" ta sanar da kama wasu matasa 15 da suka bayyana cewa 'yan 'luwadi' ne.

Da yake tabbatar da kama matasan, mataimakin kwamandan Hisbah mai kula da aiyuka na musamman, Muhammad Al-Bakary, ya ce matasan da suka kama suna shirya biki na matasa masu sha'awar jinsi ne.

Ya kara da cewa dakarun hukumar Hisbah sun kai samame gidan da matasan da suka shirya bikin murnar kammala karatun Jami'a a wani gida dake unguwar Sabuwar Gandu a Kano.

Ya ce wadanda suka shirya bikin matasa ne dake murnar kammala karatu daga wata babbar makarantar gaba da sakandire dake Kano.

DUBA WANNAN: Sunaye: Ganduje ya nada sabbin hadimai 17

Ya ce bayanan sirri da hukumar Hisbah ta samu sun tabbatar mata da cewa matasan sun shirya bikin ne musamman domin masu soyayya da jinsunsu su zo da masoyansu.

Al-Bakary ya ce yanzu haka matasan da suka kama suna karbar horo na musamman domin su sauya halayyarsu.

Kazalika, ya bayyana cewa a kalla matasa 50 ne a wurin bikin yayin da jami'an Hisbah suka dira wurin, amma duk suka gudu sai 15 aka kama.

A shekarar 2014 ne tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya rattaba hannu a kan dokar da majalisa ta zartar a kan masu soyayya da auren jinsi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel