Hatsarin "Gas" a Kaduna: Shugaban hukumar NAEC, Farfesa Malam, ya mutu

Hatsarin "Gas" a Kaduna: Shugaban hukumar NAEC, Farfesa Malam, ya mutu

Shugaban hukumar NAEC (Nigeria Atomic Energy Commission), Simon Mallam, yana daya daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin iskar gas ta aka yi jiya a garin Kaduna a ranar Asabar, cewar wani jami'i.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, hatsarin ya auku ne da karfe 2 na yammacin ranar Asabar a kan titin Kachia dake Anguwan Boro a Kaduna.

Mazauna yankin sun ce hatsarin ya faru ne a wani wajen siyar da gas, wanda hakan ya tsare mutane masu yawa a wajen.

Shaguna da yawa da suka hada da wajen aski, siyarda kayan ruwa, wajen siyar da kayan sanyawa da sauransu duk hatsarin ya ritsa dasu.

A ranar Asabar ne gwamnatin jihar Kaduna tace ba zata iya bayyana yawan mutanen da abun ya ritsa dasu ba har sai ta kammala bincike.

DUBA WANNAN: Hunturu: Yadda garwashin dumama daki ya halaka samari biyu

Kwamishinan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, wanda ya saki rahoton a ranar Asabar, bai dauki kiran wayar da aka yi masa ba a ranar Lahadi.

Amma kuma, a jawabin kakakin majalisar wakilai na tarayya na ranar Lahadi, yace hatsarin "Ya ritsa da mutane masu tarin yawa kuma yayi ajalin mutane da suka hada da shugaban hukumar NAEC, Farfesa Simon P. Mallam. Hakazalika ya kawo asarar dukiyoyin miliyoyin naira."

Gbajabiamila a yayin jajanta wa ga wadanda lamarin ya ritsa dasu yace, "Ina jaje tare da ta'aziyya ga gwamnatin jihar, iyalan wadanda suka yi rai da kuma wadanda suka rasu a hatsarin iskar gas da aka yi a jihar Kaduna."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel