Dare daya Allah kanyi Bature: Mutane sun hadawa Magajiya Danbatta taimakon Naira Miliyan 5 sanadiyyar Ja'afar Ja'afar

Dare daya Allah kanyi Bature: Mutane sun hadawa Magajiya Danbatta taimakon Naira Miliyan 5 sanadiyyar Ja'afar Ja'afar

- Wani kwamiti da fitaccen dan jarida, Jaafar Jaafar ya kafa, ya samu tallafin makuden kudi har naira miliyan biyar da doriya

- Ya kafa kwamitin don tallafawa tsohuwar mawakiya, Magajiya Danbatta bayan da ya gano ta a wani hali a garin makoda

- Mutane da yawa sun tallafa inda aka yi mata siye-siyen abubuwan bukatar yau da kullum

Wani kwamiti da fitaccen dan jarida Jaafar Jaafar ya kafa ya yi kasafin zunzurutun kudi har naira miliyan biyar domin inganta rayuwar shahararriyar zabiyar nan Magajiya Dambatta.

Idan baku manta ba, Jafar ya gano zabiyar na cikin halin kaka-ni-ka-yi a garin Makoda don kuwa har bara take yi. Dan jaridar tare da taimakon wasu abokanshi, sun kafa gidauniyar tallafi don wannan tsohuwar mawakiyar.

A halin yanzu, wannan gidauniyar ta samu tallafin da ya kai har naira miliyan biyar. Jafar ya bayyana cewa mutane 576 ne suka bada gudunmawar wannan makuden kudade. Ya kara da bayyana cewa, akwai mutum daya da ya bada har naira miliyan daya da rabi da kuma wanda ya bada naira dubu dari biyu.

Dan jaridar ya bayyana cewa sun ziyarci tsohuwar mawakiyar tare da bayyana mata abinda aka tara da kuma abinda suke da burin yi dashi. Tayi godiya ga duk wanda ya taimaka ta kowanne fanni don bada agaji gareta.

Bayan dubawar da wani likita mai suna Dakta Kabir Abdulssalam yayi, yace akwai bukatar a mika ta asibiti don a kara bincikar lafiyarta tare da magance wannan cutar makantar dake damunta.

A halin yanzu, ‘yan kwamitin sun sa dillalai su nemo filin siyarwa inda za a gina mata gida ko kuma gidan siyarwa don a siya mata.

KU KARANTA: Kuda wajen kwadayi: Budurwa ta goge lambar wani mutumi bayan yayi kuskuren tura mata Naira miliyan 1 cikin asusunta

Bayan nan, kwamitin yayi mata siye-siyen kayan da take bukata na amfanin rayuwa da suka hada da bargo, darduma, hijabai, rigunan sanyi, safuna, hulunan sanyi, shinkafa, macaroni, taliya, man shafawa, takalma, zannuwa, sabulai da sauransu.

Akwai kuma kiyasin kudin da aka ware za a dinga bata duk wata tare da jimillarshi na shekara.

Jaafar ya bayyana cewa ko ƙwandala kwamitin su ya kashe kan wannan hidima, to zai yi bayani a kan ta, duk duniya ta gani.

A kafafen soshiyal midiya dai ana ci gaba da yi wa su Jaafar ruwan yabo da addu'ar Allah ya biya su ladar wannan namijin ƙoƙari da su ka yi na ceto rayuwar Magajiya Ɗambatta daga halin ƙunci da ta shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel