Yan Najeriya sun koka kan yadda daliban kwalejin NDA ke cin zarafin matafiya suna tare hanya

Yan Najeriya sun koka kan yadda daliban kwalejin NDA ke cin zarafin matafiya suna tare hanya

Yan Najeriya kafafaen sadarwar zamani sun bayyana bakin cikinsu gami da damuwar yadda daliban kwalejin horas da hafsoshin Sojin Najeriya, NDA, suke tare manyan hanyoyi tare da muzguna ma matafiya a duk fadin Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito wani bidiyon dake yawo a kafafen sadarwa da jaridar The Herald ta daura ya nuna yadda daliban su biyar sanye da kayan Sojoji suka tare hanya, wanda hakan ya janyo cunkoson ababen hawa a wani babban titi.

KU KARANTA: Kisan kwamandan Sojan Iran: Ayatollahi Khameini ya sanar da sabon babban kwamanda

Wannan lamari ya zama tamkar al’ada ne ga daliban, inda suke kiransa da Plumming 101, kuma suna yinsa ne a duk lokacin hutun Kirismeti ko sabuwar shekara. A cikin wannan bidiyo an hangi daliban suna rawa a kan titi, suna fareti, sauran kuma suna zagin matafiya dake neman a basu hanya su wuce.

An jiyo daya daga cikin daliban yana cewa: “Babu abin da zasu iya, Ubansu! Babu da zasu iya, dole ne su jira mu, ina take ne, ina take ne? haka nake so, zo mu tafi, wani shegen ne yake danna hon? Kai shege ne? Ubanka!”

A wani bidiyo na biyu kuma an hangi daliban sun tare babban shataletalen Leventis na Kaduna, suka hada cunkoson ababen hawa.

Yan Najeriya sun koka kan yadda daliban kwalejin NDA ke cin zarafin matafiya sun tare hanya
Daliban
Asali: Facebook

Sai dai yan Najeriya da dama sun koka, inda wani mai suna @Fieldaffidavit yace yadda gwamnatin Najeriya ke wulakanta doka ne yasa daliban ma samun yancin cin zarafin yan Najeriya. Shi ma wani @WaleAkinro yace yadda daliban NDA ke wulakanci ya nuna NDA ba ta tsari.

@kennygee_70 kuma cewa ya yi: “Ina fatan rundunar Sojan kasa za ta hukunta daliban nan, Sojojinmu suna da kwarewa, ba kamar yan iskan yaran nan ba dake nuna isa a kan babban hanyar. Daliban yau su ke zama hafsan Soja a gobe.”

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi mai magana da yawun kwalejin NDA, Manjo Abubakar Abdullahi game da bidiyon, sai yace: ‘Don Allah a bani lokaci, zan mayar da martani.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel