Dan Kwakwasiya ne ya kirkiro labarin auren Buhari da Sadiya - DSS

Dan Kwakwasiya ne ya kirkiro labarin auren Buhari da Sadiya - DSS

Hukumar tsaron farin kaya wato DSS a ranar Juma'a ta damke mutumin da ake zargi da kirkiran bidiyon auren karya tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da ministan walwala da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq.

Yayinda aka bayyana matashin a hedkwatan hukumar dake Abuja, kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bayyana cewa matashin ya amince da kirkiran bidiyon da rabawa kuma dan kungiyar Kwankwasiyya.

Peter Afunanya, an kaddamar da bincike ne kan lamarin lokacin da ministar kudi, Zainab Shamsuna, ta shigar da kara.

Dan Kwakwasiya ne ya kirkiro labarin auren Buhari da Sadiya - DSS
Dan Kwakwasiya ne ya kirkiro labarin auren Buhari da Sadiya - DSS
Asali: Facebook

Yace: "A shekarar 2019, tsakanin watan Agusta da Oktoba, wata bidiyon sharri ta bayyana a fadin Najeriya da ke nuna cewa shugaban kasa na shirin aure da daya daga cikin ministocinsa."

"Ta farko itace ministar Ilimi, Hajiya Zainab Ahmad sannan kuma ministar walwala da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Farouq."

"Sunansa Kabiru Mohammed. Dan asalin jihar Kano ne, Yana da shekaru 32. Yayi karatun difloma a ilmin Hausa da Fulfulde a kwalejin ilimin tarayya ta Kano."

"Ya tona asirin kansa kuma bincike ya nuna dukkan yadda suka hada bidiyoyin da yadawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel