Na shiga karuwanci ne saboda ita ka dai ce hanyar da zan iya samun kudi - Facardi

Na shiga karuwanci ne saboda ita ka dai ce hanyar da zan iya samun kudi - Facardi

- Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani a kasar Ghana, Queen Facardi ta bayyana cewa ita karuwa ce

- Budurwar ta bayyana dalilinta na fadawa wannan sana'ar a wani shiri mai suna The Delay Show

- Kamar yadda ta ce, ta fada harkar karuwanci ne saboda lalacinta kuma ba zata iya aiki ba

Akwai alamun dake nuna cewa wannan sabuwar shekarar zata fara da kyau, don wasu sun bude cikinsu ba tare da yin karya ko kunyar halin da suke ciki ba. Mata da yawa a yanzu na tunkahon cewa basu dogara da maza ba kuma guminsu suke nema ba tare da sa hannun wani namiji ba.

Amma fa hakan ga wasu matan ne, banda wasu da suka dogara kacokan a kan mazan.

Cikin kwanakin nan ne wata sananniyar ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani a kasar Ghana, Queen Farcadi, ta shiga kanun labarai bayan da ta bayyana aikin da takeyi kuma da dalilinta.

Facardi dai karuwa ce kuma bata ji nauyin sanar da hakan ba a yayin wata tattaunawa da aka yi da ita a shirin The Delay Show.

KU KARANTA: Allah Sarki: Wata mata mai tsohon ciki ta mutu bayan maciji ya sare ta a cikin bandaki a Kaduna

Kamar yadda ta sanar, bata fada karuwanci ba saboda wani ya ja ta. Tace ta fada karuwanci ne saboda lalacinta kuma ba zata iya aiki ba.

A kalamanta: "Na yanke hukuncin amfani da jikina tunda ni malalaciya ce. Ina amfani da jikina ne don samun abinda nake so."

Facardi ta bayyana cewa, bata taba gwada yin aiki ba saboda ta gano babu abincinta a nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel