Kisan kwamandan Iran: Amurka ta umurci dukkan yan kasarta dake Iraqi su fita da wur-wuri

Kisan kwamandan Iran: Amurka ta umurci dukkan yan kasarta dake Iraqi su fita da wur-wuri

Amurka ta umurci dukkan yan kasarta dake zaune a kasar Iraqi su fita da wur-wuri saboda gudun hari daga kasar Iran. Al-Jazeera ta bada rahoto.

Ofishin jakadancin Amurka dake Iraqi ta yi gargadin ne da safiyar Juma'a, yan sa'o'i bayan Amurka ya hallaka babban kwamdandan Sojin Iran, Qassem Soleimani.

Kasar Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatar hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Hedkwatar Sojin Amurkan ta ce shugaban kasa, Donald Trump, ne ya bada umurnin kashe kwamandojin biyu dake shirin kai hari ofishin jakadancin Amurka a Iraqi.

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya bayyana cewa kasar Iran da abokanta za su mayar da martani mai zafi kan ta'addancin Amurka na kisan kwamandanta.

Hakazalika, shugaban koli na Iran, Ayatollah Ali Khameini, ya sanar da cewa za'a kwashe kwanaki uku ana zaman makoki kuma sai an mayar da martani mai tsauri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel